160610-bikin-gargajiya-na-Duanwu-na-Sinawa-Lubabatu.m4a
|
Bikin Duanwu bikin gargajiya ne na Sinawa, wanda ke da dogon tarihi, domin kuwa bisa tarihi an kai shekaru kimanin dubu biyu ana gudanar da shi, kuma a kan yi wannan biki ne a ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wanda a wannan shekara ya fado a daidai ranar 20 ga watan Yuni. Ana kuma kiran bikin da sunaye iri iri, misali, bikin Duanyang, bikin watan Mayu, bikin tseren kwale-kwale da sauransu. To, shin wadanne al'adu ne ke jibantar wannan biki, kuma yaya ake gudanar da shi? Domin samun karin haske, sai a biyo mu a shirin.(Lubabatu)