Wannan shi ne karon farko da aka shirya Kwas din a kasar Sin wanda ake gudanarwa tare da hadin gwiwar sashen kula da aikin kiyayen zaman lafiya na MDD da ma'aikatar kula da harkokin tsaro ta kasar Sin.
Manyan kwararru a fannin aikin kiyaye zaman lafiya 26 daga kasashe 17 ne za su horas da kwadandoji da sojoji da ke aikin kiyaye zaman lafiya.
A yayin bikin bude kwas din, mahalartan sun tashi tsaye inda suka yi shiru domin nuna girmamawa ga sojojin da aka kashe a yayin da suke bakin aiki.
A jawabinsa yayin bikin,shugaban sashen ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD Herve Ladsous, ya yaba rawar da sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suka taka a wuraren da aka tura su. Bugu da kari, ya mika sakonsa na ta'aziya ga dakarun da suka kwanta dama da wadanda suka jikkata a yayin da suke gudanar da wannan aiki.(Ibrahim)