in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asalin Hausa
2016-06-04 12:53:47 cri

Sanin kowa ne cewar, kowace al'umma da kuma kowace kasa a duniyar nan tamu, tana da tarihin asalin kafuwarta, al'adunta da kuma dabi'unta wadanda take alfahari da su. Su ne kuma suke bambanta kasa ko al'umma. To, in mun yi zancen asalin tarihin Hausa, to, ma iya cewa kasar Daura na da matsayi mai muhimmanci a tarihin kasar Hausa.

To, A wannan makon shirin Allah daya gari Bambam zai yi nazari ne kan hirar da wakilinmu Murtala ya yi da Malam Ibrahim Hamisu mai ba da shawara kan yada labarai, tarihi da karbar baki ga mai martaba sarkin Daura game da tarihin Hausa. Bugu da kari,shirin zai duba dalilin zuwan Bayajida garin na Daura mutumin da wasu masana da bincike suke bayyanawa a matsayin asalin Kalmar Hausa. Koda yake wasu na ganin dukkan wadannan bayanai tatsuniya ce. Amma Malam Ibrahim Hamisu ya yi bayani game da shaidun da ke tabbatar da asalin Hausa da sauran muhimman bayanai duk a cikin wannan shiri.

Da fatan za ku kasance da mu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China