in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin kafofin sadarwa ga ci gaban duniya
2016-06-03 15:15:52 cri

A ranar 2 ga watan Yunin shekarar 1875 ne wasu mutane biyu wato Alexander Graham Bell da abokin aikinsa Thomas Watson suka gano wani abu mai muhimmanci bisa kuskure a lokacin da suke aikin hada layin tangarahu.

Shi dai Bell da Watson sun gano wata hanya ta aikewa da sauti ne ta jikin waya. Daga bisani ya yi magana da abokinsa daga wani daki, abin da ya zama mafarin jin sauti ta cikin wani abu mai kama da waya daga wani daki zuwa wani daki na daban.

Sannu a hankali aka ci gaba da inganta wannan tsari, har ta kai shi ga nadar bayanin da ya rubuta, wanda ya karanta ta cikin wannan na'ura. Daga karshe, wannan ya kasance wayar tangarahu ta farko da aka kirkiro a duniya.

Sakamakon ci gaban bincike da kirkire-kirkire na masana a fannoni daga sassa daban-daban na duniya, ya sa duniya ta amfana da hanyoyi sadarwa iri daban-daban, tun daga layin tangarahu har zuwa wayar tarho, gidan waya, salula, radiyo, talabji, yanar gizo ta intanet, tauraron dan Adam, da dai sauransu.

Masana na cewa, bullar wadannan hanyoyin sadarwa sun saukaka al'amuran rayuwa tare da samar da ci gaba a dukkan fannoni. Sai dai duk da irin wadannan ci gaba da wadannan hanyoyi suka samar, masu fashin bakin a daya hannun na cewa, sun kuma haifar da wasu illoli da ba za a rasa ba. Na farko, hanyoyin sun gurbata rayuwar matasa, inda wasu ke amfani da wadannan kafofi wajen cutar da jama'a, kamar satar bayanai ta intanet, kallon hotunan batsa, nakasa bangaren tattalin arzikin kasa, cusa tsattsauran ra'ayi, kamar yadda wasu 'yan ta'addan ke amfani da wadannan kafofi wajen yada munanan akidunsu.

Masharhanta na ganin cewa, wajibi ne mahukunta su rika sanya dokoki game da yadda al'ummomin kasashensu za su rika cin gajiyar wadannan kafofin sadarwa ba tare da sun kawo illa ga tsaron kasa da kuma tsarin zaman takewar al'umma ba. (Saminu, Ada, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China