in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar Sin ya fidda takardar bayani game da yanayin 'yancin addinai a jihar Xinjiang
2016-06-02 13:56:58 cri

A yau Alhamis ne ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda wata takardar bayani, game da 'yancin addinai a jihar Xinjiang mai cin gashin kan ta.

A cikin takardar, an nuna cewa, tarihi ya shaida bukatar raya addinai bisa yanayin zamantakewar al'umma, kuma akwai wajibcin nacewa manufofi bisa yanayin da kasar ke ciki, kana ya zama dole masu bin addinai daban daban su zauna tare cikin jituwa. Kaza lika ya zama dole a yi biyayya ga manufar koyi da juna, da zama cikin jituwa, da bin addinai cikin 'yanci, don kaucewa yake-yake da rikici.

Har wa yau takardar ta nuna cewa, tun kafuwar sabuwar kasar Sin, ana gudanar da manufar bin addinai cikin 'yanci a jihar Xinjiang yadda ya kamata, ana kuma girmama addinai cikin 'yanci, kana masu bin mabambantan addinai suna taka muhimmiyar rawa, wajen sa kaimi ga tattalin arziki da raya zamantakewar al'umma. Haka kuma, ana dakile masu bin tsattsauran ra'ayi a yankin.

Bugu da kari, takardar bayanan ta nuna cewa, Sin na tsayawa tsayin daka wajen raya harkokin addinai bisa yanayin da kasar ke ciki. Kana ta dage wajen raya addinai, don haka bai kamata kungiyoyin kasashen waje, ko na sauran mutane su rika kutse cikin harkokin addinai na kasar Sin ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China