in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Afrika ta Kudu ya yi kira da a inganta hadin gwiwa game da makamashin karafa a tsakanin kasashen biyu
2016-06-01 15:27:04 cri

A ranar 26 ga wata ne, jakadan Sin da ke kasar Afrika ta Kudu Tian Xuejun ya zanta da manema labaru na kasar Afrika ta Kudu game da hadin gwiwar makamashin karafa a tsakanin kasashen Sin da Afrika ta Kudu, inda ya nazarci dalilin da ya sa aka samu rarar makamashin karafa a duniya, ya kuma bayyana matakan da Sin ta dauka game da aiwatar da manufar fitar da makamashin karafa zuwa kasashen waje.

Don haka, ya yi kira ga gwamnatoci da masana'antu na kasashen biyu da su inganta hadin gwiwa a fannin makamashin karafa, don cimma moriyar juna.

Game da wasu tsirarrun mutane da ke shaci fadin cewar, wai ya kamata Sin ta dauki alhakin rarar makamashin karafa da ake fama da shi a duniya. Jakadan Tian ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka samu rarar makamashin karafa a duniya, ba laifin kasar sin ba ne, kasashen Turai da Amurka su ma suna fama da matsalar rarar makamashin. Baya ga kasancewa kasar da ke kera karafa a duniya, kasar Sin kana kuma amfani da makamashin karafa da dama, kashi 90 cikin 100 na kayayyakin karafan da Sin ta kera, ta yi amfani da su wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Jakadan Tian ya ce, an samu rarar makamashin karafa a duniya ne sabo da tsarin wannan sana'a, kuma an fuskanci wannan matsala ce a wani lokaci a baya. Bayan da rikicin kudi na duniya ya barke, an dauki tsawon lokaci ba a samu karuwar tattalin arziki ba, lamarin da ya haddasa matsalar rashin biyan bukatun kasuwannin sayar da karafa a duniya, amma a lokacin da tattalin arzikin kasashe da dama ya bunkasa, sun kera makamashin karafa fiye da kima, sabo da haka, aka samu rarar karafa a duniya. Ban da wannan kuma, sha'anin karafa na wasu kasashe masu wadata, ba su da fiffiko, amma gwamnatocin kasashensu sun ci gaba da kiyaye hako makamashin karafa don tabbatar da samar da guraben aikin yi, wannan ya tsananta matsalar kera karafa fiye da kima a duniya.

Ya jaddada cewa, muddin ana bukatar warware wannan matsala, bai kamata a zargi juna ko daina sauke nauyin da ya kamata ba, idan ba haka ba, ba za a warware matsalar kiyaye ciniki na kasashen ba, a maimakon hakan, zai kawo illa ga tsarin cinikin kasa da kasa.

Jakadan Tian ya bayyana matakan da gwamnatin Sin ta dauka wajen warware matsalar kera karafa fiye da kima a kasar. Ya ce, yanzu, Sin na gaggauta yin kwaskwarima game da tsarin samar da kayayyaki a kasar, wani muhimmin mataki na warware matsalar kera karafa fiye da kima a kasar. A cikin shekaru 3 da suka gabata, Sin ta daina kera karafa da yawansu da ya kai sama da Tan miliyan 90. A cikin shekaru da dama masu zuwa, Sin ta yi shirin saka rage samar da karafan da yawansu ya kai Tan miliyan 100 zuwa 150.

Don ci gaba da kyautata sana'ar kera karafa a kasar Sin, gwamnatin kasar ta bukaci sassan daban daban na kasar da su daina bude sabbin masana'antun kera karafa a kasar, kuma masana'antun ba za su kara kera karafa ba, kana kuma ya kamata a gudanar da manufar kiyaye muhalli, da tabbatar da tsaro, da inganci, don ci gaba da rage masana'antun da ba su dace ba.

Yayin da jakadan yake zantawa da manema labaru kan shirin gwamnatin Sin na samar da kudin bonus game da fitar da karafa zuwa kasashen waje, ta yadda za ta yi babakere a kasashen waje ta fuskar farashi mai rahusa, sabo da haka, lamarin ya haifar da illa sosai game da sha'anin narkar da karafa, jakadan Tian ya ce, a matsayinta na mambar kungiyar cinikayya ta kasa da kasa wato WTO, kasar Sin ta martaba tsarin cinikin kasa da kasa, ba ta ba da kudin rangwame game da fitar da karafa zuwa kasashen waje ba. A maimakon hakan, Sin ta sanya haraji game da fitar da kayayyakin karafa zuwa kasashen waje, abin da ba a taba yi ba a sauran kasashen da ke hako karafa ba.

Jakadan Tian ya ce, kasar Sin ta yi fice ne wajen fitar da kayayyakin karafa, saboda masana'antun Sin suna da fiffiko a fannoni 'yan kwadago, da ayyuka, da fasahohi, da samar da kayayyaki. A sa'i daya kuma, farashin muhimman kayayyakin da duniya ke bukata suna da rahusa, abun da ya kara karya farashin karafa.

Tian Xuejun ya yi nuni da cewa, wasu kasashe sun nuna cewa, Sin ta yi babakere wajen fitar da karafa zuwa kasashen waje ne, sabo da sun tsara tsarin farashinsu bisa la'akari da yanayi kasashensu, sannan ba su bayyana yanayin da kayayyakin karafa ke ciki a kasar Sin ba. Bisa yarjejeniyar shigar Sin a cikin kungiyar WTO, bai kamata mambobin kungiyar WTO su binciki Sin game da babakeren da ta yi a kasuwannin karafa na duniya ba.

A game da makomar hadin gwiwa game da raya sha'anin karafa a tsakanin kasashen Sin da Afrika ta Kudu kuwa, jakadan Tian ya ce, a halin da ake ciki yanzu, kasashen Afrika na gaggauta raya masana'antu, kuma ana matukar bukatan makamashin karafa. A halin da ake ciki kuma, taron koli na dandalin tattaunawar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Jonhanesburg, ya kara karfafa wani yanayi na hadin gwiwa kan wasu fannoni da ababen more rayuwa,lamarin da ya kirkiro wasu bukatu game da kasuwannin karafa a nahiyar Afrika. Sha'anin karafa na Afrika ta Kudu na da makoma mai kyau, kuma Sin tana da kwarewar fasahohi da kudade, ya kamata kasashen Sin da Afrika ta Kudu su yi hadin gwiwa tare don raya kasuwannin Afrika.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China