in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudu ya dace da moriyar bangarori daban daban, in ji jami'in tsaron Sin
2016-05-27 14:34:31 cri

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Yang Yujun, ya ce ka'idar tsaro da sojojin kasar Sin da na Amurka suka tsara dangane da matakan da za a dauka bayan gamuwar jiragen saman kasashen biyu, da kuma gamuwar jiragen ruwansu, ka'idar fasaha ce kawai, kuma dakatar da binciken da kasar Amurka ta yi a yankin tekun kudu ita ce hanya mafi dacewa, ta daidaita batun yankin tekun kudu.

Yang Yujun ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru game da batun shigar jiragen saman kasar Amurka yankin tekun kudu, a gun taron manema labaru da aka gudanar a jiya Alhamis. Mr. Yang ya ce kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudu ya dace da moriyar bangarori daban daban.

Ma'aikatar tsaro ta kasar Sin ta yi taron manema labaru a jiya Alhamis da yamma, domin mai da martani ga batutuwan soja wadanda suka fi jawo hankulan mutane a halin yanzu.

A kwanan baya, an labarta cewa, ma'aikatar tsaro ta kasar Amurka ta zargi jiragen saman sojan kasar Sin guda 2, da su hana wani jirgin saman leken asiri na kasar Amurka ya ratsa yankin tekun kudu ta hanya maras dacewa.

A gabanin haka, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta mai da martani kan wannan batu. A gun taron manema labarun na jiya, kakakin ma'aikatar tsaro ta kasar Sin Yang Yujun ya bayyana cewa, zargin da kasar Amurka ta yi ba shi da ma'ana,

"Jirgin saman soja na kasar Amurka ya yi aikin leken asiri ne a yankin sama da ke kusa da tsibirin Hainandao na kasar Sin, don haka jiragen saman sojan kasar Sin sun duba asalinsu, hakan ya dace da ka'idar tsaro da kasashen Sin da Amurka suka tsara a baya. A zahiri, kasar Amurka tana nufin boye hakikanin lamarin ne, domin jawo hankulan duniya kan nisan dake tsakanin jiragen saman kasashen biyu, a maimakon kan aikin leke asirin da jiragen sama da na ruwa na kasar Amurka suka dade suna gudanar a kusa da yankunan Sin, aikin da ya haifar da matsalar aikin soja a tsakanin kasashen 2, kana ya haddasa hadari a tsakanin kasashen 2 a teku da sama. Kasar Sin ta nemi kasar Amurka da ta daina leken asiri kurkusa, domin kaucewa sake faruwar irin wannan lamari."

Mr. Yang Yujun ya kara da cewa, kasar Sin tana da ikon kaiwa ga jerin tsibiran tekun kudu, da kuma yankunan tekun dake kusa da su. Kana Sin ta nace ga daidaita batutuwa ta hanyar shawarwari tare da sauran kasashe bisa tarihi da dokokin duniya. Ya ce, kasar Sin tana tsaya wa tsayin daka kan kare ikon mulkin kai da moriyarta a yankin teku. Yang ya ce,

"Wasu kasashen da ba ruwansu da batun tekun kudu na nuna karfin sojansu a yankin, hakan da ya fi haifar da cikas matuka ga zaman lafiyar yankin. Kasar Sin ta nemi wadannan kasashe da su daina gudanar da irin wadannan ayyuka. Kiyaye zaman lafiya a yankin tekun kudu ya dace da moriyar bangarori daban daban baki daya."

A jiya Alhamis ne dai aka cika shekara daya da bude shafin ma'aikatar tsaron kasar Sin kan internet na Microblog, da Wechat. Mr. Yang ya bayyana ya amsa tambayoyin masu amfani da internet a Wechat domin taya murnar wannan rana. Wani ya yi tambayar cewa, "Duk da kasar Sin tana da makaman soja masu karfi, amma sojojinta ba su shiga yake-yake ba cikin shekaru fiye da 10, shin sojojin na Sin na da karfin yaki a yayin da halin dake kewayan kasar ya kara tsananta?

Mr. Yang ya ce, lallai sojojin Sin ba su shiga yake-yake ba a tsawon shekaru fiye da goma, sabo da kasar Sin ta nace ga neman bunkasuwa ta hanyar lumana, amma sojojin ta na da cikakken karfi.

"Duk da cewar, galibin sojojinmu ba su taba shiga yaki ba, amma suna cin jarrabawar horo a lokacin da suke kiyaye mulkin kan kasa, da yaki da ta'addanci, da ceton mutane daga bala'u, da kiyaye zaman lafiya a ketare. Musamman na tun daga babban taron wakilan JKS karo na 18, mun tsaurara horar da sojoji kamar yadda suke yi a yake-yake, ta haka, karfin sojojinmu ya samu karfafuwa sosai. Baya ga karfin shiga yake-yake, sojojinmu suna kuma da kwarewa sosai."(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China