in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya
2016-05-27 08:22:36 cri

Ranar 29 ga watan Mayun kowace shekara, rana ce da MDD ta kebe a matsayin ranar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD. An kebe ranar ce domin karrama ma'aikatan kiyaye zaman lafiya da suka kwanta dama a lokacin da suke bakin aiki, da kuma wadanda suka nuna kwarewa, da sadaukar da kai da kuma aiki tukuru a lokacin da suke gudanar da wannan aiki.

An fara aikin wanzar da zaman lafiya na MDD ne a shekara ta 1948, lokacin da kwamitin sulhu na MDD ya ba da umarnin tura sojojin sa ido na MDD zuwa yankin gabas ta tsakiya. Kuma tun wancan lokaci, MDD ta tura ma'aikatan wanzar da zaman lafiya 69, kuma 56 daga cikinsu tun a shekara 1988.

A 'yan shekarun da suka gabata dubban daruruwan sojoji da dubun-dubatar 'yan sanda da sauran fararen hula daga sama da kasashe 120, ciki har da kasar Sin da wasu kasashen Afirka ne suka shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD a sassa daban-daban na duniya ciki har da kasashen Afirka.

Bayanai na nuna cewa, sama da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD 3,326 daga kasashe 120 ne suka rasa rayukansu a lokacin da suke gudanar da wannan aiki.

Tun bayan yakin cacar-baka, MDD ta kara yawan ayyukanta na wanzar da zaman lafiyta a sassa daban-daban na duniya. Amma duk da wannan mataki na shimfida zaman lafiya, har yanzu ana fama da yake-yake da tashin hankali a wasu sassan duniya, lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyin jama'a, baya ga miliyoyin da suka rasa matsugunansu.

Bugu da kari, ana kara fuskantar barazana da kalubale wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya. Don haka, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya tabbatar da cewa, MDD za ta ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron fararen hula, hana abkuwar yake-yake, da samar da sharadi don shimfida zaman lafiya mai dorewa.

Masu sharhi na ganin cewa, wajibi ne ma'aikatan da ke gudanar da irin wadannan ayyuka su kiyaye dokokin MDD kana a rika hukunta wadanda suka saba ka'idojin aikin kamar yadda doka ta tanada don gudun zubar da kima da martabar MDD, Sannan a karrama sojojin kasashen da suka taka rawar gani a lokacin da suke gudanar da ayyukansu, kamar yadda aka yiwa tawagar kasar Sin a kasar Mali a baya-bayan nan ta yadda zai kasance abin misali ga sauran kasashen duniya. (Saminu, Ada, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China