in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Miliyoyin 'yan al'ummar Zimbabwe sun yi zanga-zangar goyon bayan Robert Mugabe
2016-05-26 14:14:10 cri

A jiya Laraba ne yayin bikin ranar Afrika, miliyoyi al'ummar kasar Zimbabwe suka gudanar da zanga-zanga a birnin Harare, fadar mulkin kasar, don nuna goyon bayan su ga shugaba Robert Mugabe, bisa burin sa na shiga babban zaben shugabancin kasar a shekarar 2018.

Da sanyin safiyar jiya Laraba ne jam'iyyar kawancen dimokuradiyya ta (ZANU-PF) mai mulkin kasar, ta tattara mutane masu dimbin yawa daga manyan jihohi 10 domin gudanar da jerin gwano a birnin Harare, wadannan mutane sun sanya tufafin dake da hoton Mugabe tare da rike da tutoci, kuma sun yi tattaki kan manyan titunan birnin Harare zuwa filin taro ne Mugabe dake cibiyar birnin. Ban da haka kuma, masu zanga-zangar sun taru a ofishin jakadancin kasar Afrika ta kudu, da dakin motsa jiki na Rufaro, da kuma wani dakin motsa jiki na kasar.

Mataimakin babban sakataren kungiyar matasan kishin kasar ta Zimbabwe Cde Kudzai Chipanga ya ba da jawabi, inda ya yi alkawari cewa, kungiyarsa za ta goyi bayan Robert Mugabe. Ya ce, shi ne 'dan takara daya tilo ga jam'iyyar a babban zaben na shekarar 2018. Wani malamin da ya zo daga birnin Harare ya bayyana cewa, ya isa filin Mugabe ne domin taya murnar ranar Afrika, da kuma nuna goyon baya ga shugaba Mugabe. A game da halin tattalin arziki maras kyau da kasar Zimbabwe ke ciki, yana ganin cewa, wannan shi ne batun da kowace kasa mai tasowa za ta yi fama da shi wajen raya tattalin arziki. "Sabo da muna cikin takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kakkaba mana, shi ya sa, tattalin arzikin mu bai samu bunkasuwa sosai ba, amma na yi imani da cewa, za a samu kyautatuwa a nan gaba a karkashin jagorancin shugaban Mugabe."

A watan Maris na wannan shekara, Robert Mugabe ya gaya wa manema labaru cewa, idan yana da lafiya, zai shiga babban zaben kasar na shekarar 2018 bisa matsayin 'dan takara na jam'iyyar ZANU-PF. A watan da ya gabata kuma, magoya bayan jam'iyyar adawa ta MDC sama da dubu daya sun taru don nuna adawa ga wannan lamari, kana sun yi kira ga Robert Mugabe da ya bar kujerar mulkin kasar.

A jiya Laraba, Robert Mugabe ya zargi jam'iyyar adawa a cikin jawabinsa, yana mai cewa, "Yau, mun zo nan don kara yin hadin kai, muna iya kalubalantar mutanen da suka zarge mu. Ba su ji dadi ba sabo da ganin mutane masu dimbin yawa sun taru a nan. Muna son cimma burin kafa kyakkyawar makoma a kasar Zimbabwe, ba kamar yadda jam'iyyar adawa take da niyya ba, tana son ganin munanan abubuwa sun faru a kasar mu."

Ban da haka kuma, Robert Mugabe ya yi zargin cewa, "Wasu 'yan jam'iyyar dake mulkin kasar ba su basira ko kadan, sun bayyana kan su da shiga wata karamar kungiya ta musamman, wasu daga cikinsu sojojin da suka ritaya ne, abin da suke yi ba shi da ma'ana, sabo da karamar kungiya ba za ta kasance a cikin jam'iyyar ba. Wadannan mutane suna aiki ne a cikin kungiyar su kadai, domin jam'iyyar ZANU-PF daya ce tak a wannan kasa."

Kakakin jam'iyyar adawa ta MDC Obert Gutu ya bayyana cewa, jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar ta yi zanga-zanga a jiya, domin kawar da hankulan mutane. A halin yanzu, galibin al'ummar kasar Zimbabwe na fama da talauci mai tsanani, ba su jin dadin zaman rayuwarsu ba, jam'iyyar tana fatan kawar da hankulan mutane daga tabarbarewar tattalin arzikin kasar, tare da gamsar da Mugabe mai son kai.

Tun daga watan Maris na wannan shekara, ake ta fama da matsalar karancin kudade a kasar Zimbabwe, kana tsoffin sojoji da mutanen da suka yi ritaya ba su iya samun albashi daga bankuna, yayin da na'urorin ATM su kan yi karancin kudade. Domin sassauta karancin kudade, shugaban bankin tsakiya na kasar Zimbabwe ya sanar a ranar 4 ga watan Mayu cewa, kasar Zimbabwe za ta samar da takardun bashi da yawansu zai kai dalar Amurka miliyan 200, kana za ta kayyade yawan kudaden da mutanen za su iya cira daga bankuna.

A daya hannun kuma asusun IMF ya ba da sanarwa a wannan rana cewa, tattalin arzikin kasar Zimbabwe na fama da hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani. Ya kuma yi hasashe cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Zimbabwe a bana zai kai kashi 1.5 cikin dari, wanda zai yi daidai da na shekarar 2015.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China