160525-hadin-gwiwa-sada-zumunta-bako.m4a
|
Su Jian ya ce, ko da yake, akwai nisa tsakanin kasashen Sin da Mozambique, amma tarihi ya nuna cewa, akwai daddaden mu'amala a tsakanin kasashen biyu, da sada zumunta a tsakanin jama'arsu. A zamanin daular Ming ta kasar Sin, ayarin jiragen ruwa na Sin karkashin shugabancin Zheng He ya isa kasar Mozambique. A ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 1975 ne, kasashen Sin da Mozambique suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu. A cikin shekaru 41 da suka gabata, kasashen biyu sun inganta amincewar juna a fannin siyasa, kuma sun taimakawa juna cikin aminci game da manyan lamuran duniya, kana sun karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakaninsu, sun kuma kara mu'amalar jama'a a tsakaninsu, yanzu, kasashen biyu sun zama hakikanin abokai, 'yan uwa, kuma aminai.
Tun daga shekarar 1975 zuwa wannan lokaci , duk wani shugaban kasar Mozambique ya kan kawo ziyara kasar Sin, kuma suna nuna kaunar musamman ga kasar. A shekaru 60 na karnin da ya wuce, yayin da jama'ar kasar Mozambique suke fafutukar neman 'yancin kai, shugaban Nyusi ya taba karatu a sansanin Nacingui da ke kasar Tanzaniya, kuma ya kulla zumunci sosai da kwararru a wurin. A shekarar 2015, bayan da ya zama shugaban kasar, ya sha bayyanawa cewa, Sin ta fara kulla huldar diplomasiyya da kasar Mozambique.
Su Jian ya ce, wannan shi ne karo na farko da shugaban Nyusi ya kawo ziyara kasar Sin tun bayan da ya hau karagar milkin kasar, a yayin ziyararsa, ya yi shawarwari da shugabannin kasar Sin game da kafa amincewar juna a fannin siyasa, da inganta hakikanin hadin gwiwa daga dukkan fannoni, da mu'amala mai zurfi game da manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya, da fasahohin da Sin da yi amfani da su wajen tafiyar da harkokin mulki, da daukar matakai don cimma nasarorin da aka samu a yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC da aka yi a birnin Johannesburg, kana ya ziyarci lardunan Jiangsu da Shandong, wannan tafiya na da ma'anar musamman wajen kyautata dangantakar sada zumunta dake tsakanin kasashen Sin da Mozambique.
A cikin 'yan shekarun nan, tattalin arzikin kasar Mozambique ya samu bunkasuwa sosai, kasar Mozambique ta nuna wani abun misali mai kyau ga sauran kasashen Afrika wajen raya tattalin arziki. Su Jian ya ce, Sin ta gabatar da shirin raya kasa na Ziri Daya da Hanya Daya, yayin da kasar Mozambique ta zama kasar da ta kunshi kasashen da ke cikin wannan shiri a cikin sauran kasashen Afrika. Hadin gwiwa a fannin makamashi ya zama wani muhimmin abu wajen raya dangantakar hadin gwiwar kasashen biyu. A watan Febrairu na bana, yayin da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya ziyarci Mozambique, kasashen Sin da Mozambique sun amince da inganta hadin gwiwa a fannin makamashi, kana bangarorin biyu sun amince da mayar da iskar gas da sha'anin kirkire-kirkire don su zama muhimman sassan da kasashe biyu za su raya, kana kasashen biyu za su raya muhimman ababen more rayuwa da kyautata rayuwar jama'a da nuna goyon baya ga harkokin tattara kudade don nuna goyon bya ga hadin gwiwa a fannin makamashi a tsakaninsu.
Su Jian ya nuna cewa, ban da inganta hadin gwiwa a fannin makamashi, a cikin sabon shirin raya kasa cikin shekaru biyar masu zuwa, gwamnatin Mozambique ta nuna cewa, za ta yi kokarin raya masana'antu da inganta muhimman ababen more rayuwa, da cimma burin zamanantar da aikin gona. Akwai kuma makoma mai haske game da inganta hadin gwiwa a tsakaninsu a wadannan fannoni.
Rahotanni na nuna cewa, yanzu haka, akwai kamfanonin Sin da suka bude rassansu a Mozambique baya ga wadanda suka yi rajista kimanin 80, wadanda suka saka jari, da gudanar da gine-gine a wurin. Muhimman ayyukan da suka yi a kasar sun kunshi babbar gadar Maputo zuwa katengbe da babban filin jiragen sama na Maputo da fadar shugaban kasar, da cibiyar taron kasa da kasa ta Hisano da dai sauransu.
A cikin 'yan shekarun nan, yawan jarin da masana'antun Sin suka saka a kasar Mozambique ya samu babban ci gaba, kana masana'antun Sin da dama na kokarin lalubo sabuwar hanyar hadin gwiwa da kasar, don kara samun damar ciniki a kasar. Hakikanin hadin gwiwa ta sada zumunta a tsakaninsu zai samu babban ci gaba, kuma bangarorin biyu za su cimma moriya da samun bunkasuwa tare, kana hadin gwiwa a tsakaninsu zai zama abun koyi wajen yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.(Bako)