Wannan shiri zai kunshi fannoni 3, wato fannin kafa tsarin tattara bayanai don bambanta matsayin al'ummar kasar. Sai kuma kafa tsarin sarrafa magunguna. Na uku kuma shi ne batun kafa da kyautata tsarin mu'amalar nazarin bayanai.
Ministan kiwon lafiyar kasar Kongo (Kinshasa) Felix Kabange Numbi Mukwampa, ya bayyana cewa, yanzu haka kashi 1 cikin 4 na jama'ar kasar ne kadai ke da takardar haihuwa, abun da ke kawo matsalar rashin cikakkiyar kididdiga ta tsara wasu shirye-shiryen kiwon lafiya.
Gwamnatin Kongo (kinshasa) dai na fatan yin amfani da wannan shiri, wanda zai a gudanar cikin shekaru 4, don kyautata yanayin kiwon lafiya ta hanyar kididdigar bayanai game da al'ummar kasar, da samar da alkaluman da za a amince da su wajen tsara shirin raya kiwon lafiya na kasar daga shekarar nan ta 2016 zuwa shekarar 2020.(Bako)