in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana'antun Sin za su kara taka rawar gani wajen taimakawa kasashen Afrika
2016-05-19 09:06:30 cri

Tsohon manzon musamman na kasar Sin Liu Guijin, wanda ya kwashe shekaru 18 a kasashen Afrika, ya tattauna da mahalarta taron kolin kasa da kasa na dandalin tattaunawar tattalin arzikin Afrika wato WEF karo na 26 game da yadda za a inganta hadin gwiwa da kasashen Afrika kan fasahohin zamani da dunkulewar kasashen Afrika baki daya.

A zantawarsa da wakilinmu, Mr Liu ya ce, akwai babbar dama wajen raya nahiyar Afrika, yayin da kasashen Afrika ke raya fasahohin zamani, masana'antun Sin za su kara taka rawar a zo a gani.

Liu Guijin ya ce, salon raya kasashen Afrika ta hanyar zamani take ne mai kyau, taken taron kolin Afrika na dandalin WEF na wannan karo yana da muhimmancin sosai.

Ya ce,a kullum taron tattaunawa na WEF ya kan gabatar da sabon tunani don jaddada kirkiro da sabon tunani, a yayin taron kolin Afrika da aka yi na wannan karo, an gabatar da wannan tunani, kan yadda za a canja kasashen Afrika ta hanyar fasahohin zamani, lamarin da zai sa kaimi ga kara mu'amala tsakanin kasashen Afrika,don haka ya kamata kasashen Afrika su yi amfani da albarkatun kasa da Allah ya hore musu, ta yadda za su inganta ababen more rayuwa, da ba da hidimomi da sana'ar kirkire-kirkire.

Game da babban kalubale da kasashen Afrika suke fuskanta a yunkurin da ake yi na raya kasashen duniya ta hanyar fasahohin zamani, Mr. Liu ya ce, yanzu, ababen more rayuwa a kasashen Afrika na baya-baya, abun da ya kawo cikas game da samun bunkasuwa a wurin, game da wannan fanni, ya kamata su koyi fasahohin da Sin ta samu. Sinawa na cewa, "Idan aka samu wadata, to da farko a gina hanyoyi."Bayan da aka kyautata muhimman ababen more rayuwa a kasashen Afrika, za a iya raya nahiyar ta hanyar fasahohin zamani. A wata sabuwa kuma, a ko wace shekara, kasashen Afrika su kan samu kudin agaji da dama daga bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya, ko da yake, wadannan gudummawa sun taimakawa kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa, amma abun da ya kara kawo matsala ga kasashen Afrika wajen biyan bashi da suka ciyo daga sauran kasashen duniya. A sa'i daya kuma, kasashen Afrika na fama da karancin kwararru masu ilmi sosai, kuma muddin babu kwararru, hakika ba za a cimma burin raya nahiyar ta hanyar fasahohin zamani ba.

Sakamakon rikicin hada-hadar kudi na duniya, da raguwar farashin muhimman kayayyaki, wadannan sun taimakawa ga tafiyar hawainiya wajen raya tattalin arzikin Afrika, a cikin rahoton hasashen tattalin arziki da IMF ya fidda a ranar 3 ga wata, an rage hasashen karuwar tattalin arzikin Afrika daga kashi 4.3 cikin 100 zuwa kashi 3 cikin 100. Duk da cewa, saurin bunkasuwar da kasashen Afrika za ta samu ta fi matsaikacin karuwar tattalin arzikin duniya wato kashi 2.4 cikin 100.

Liu Guijin yana ganin cewa, kasashen Afrika na da 'yan kwadago da dama, kuma idan har aka samar musu ilmi da horo mai kyau, za a ingiza bunkasuwar kasashen Afrika.

Bisa hasashen al'ummar kasashen duniya da M.D.D. ta fidda a shekarar 2015, an ce, ya zuwa shekarar 2050, kasashen Afrika za su samu matasa 'yan shekaru 21 zuwa 24 mafiya yawa duniya.

Ban da 'yan kwadago kuma, Liu Guijin ya ce, kasashe masu wadata sun zuba kudi sosai a bangaren nazarin wasu fasahohi, kuma yanzu ana amfani da su sosai a kasashen duniya, har ma da nahiyar Afrika, abun da ya kawo fasahohin zamani ga kasashen Afrika. Alal misali, a wasu kasashen Afrika, ciki har da Rwanda da sauransu sun fara amfani da Internet na 4G.

A wasu kasashen Afrika, kuwa an cimma burin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, lamarin da ya samar da tabbaci ga samun bunkasuwar nahiyar cikin hanzari. Sai dai duk da sakamakon manyan zabe da aka gudanar a wasu kasashen Afirka da sauransu,har yanzu ana ci gaba da yake-yake da rikici a wasu kasashe, amma wadannan matsaloli ba za su ci gaba da zama ba, akasarin kasashen Afrika sun kama hanyar samun bunkasuwa yadda ya kamata.

Game da dama da kalubalen da kasashen Afrika ke fuskanta, ya kamata masana'antun Sin su taka rawar a zo a gani. Don inganta hadin gwiwa da kara mu'amala a tsakanin nahiyar, wato ya kamata a raya muhimman ababen more rayuwa da sauran fannoni dake wurin. Liu Guijin ya ce, alal misali, wasu masana'antun sadarwar Sin suna da fasahar mallakar fasaha, da kudade, da kwararru, wadannan za su taimakawa kasashen Afrika wajen raya fasahohinsu na zamani.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China