160513-Shimfida-hanyoyi-da-kyautata-zirga-zirga-na-taka-muhimmiyar-rawa-wajen-yaki-da-kangin-talauci-Lami.m4a
|
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kira taron majalisar gudanarwa ta kasar Sin a ranar 20 ga watan Afrilu, domin fara ayyukan yaki da talauci ta hanyar kafa manyan ayyukan yau da kullum na zirga-zirga da kara karfin mutanen dake wurare mafi talauci a fannin kubutar da kangin talauci. A gun wannan taro, an gabatar da cewa, kyautata tsarin zirga-zirga a tsoffin yankuna da yankunan kananan kabilu da yankunan dake iyakar kasa da kuma wuraren dake fama da talauci na da muhimmanci sosai wajen kubutar da mutane daga kangin talauci da kuma cimma daidaito a tsakanin yankuna daban daban a fannin neman samun bunkasuwa. Ban da haka kuma, taron ya tabbatar da cewa, za a kammala aikin kafa tsarin zirga-zirga mai inganci a yankunan dake fama da talauci kafin shekarar 2020.