in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Afrika na bukatar karuwar masu zuba jari na zaman kansu
2016-05-12 09:50:03 cri

Masu fashin baki sun bayyana cewa, kasashen Afrika na bukatar karin masu zuba jari domin samun habakar tattalin arzikin nahiyar.

Kwararru sun bayyana hakan ne a rana ta farkoi na taro game dandalin na kasa da kasa a game da tattalin arzikin Afrika na 2016.

Taron na tsawon kwanaki 3 karo na 26th, an bude shi ne a ranar Larabar da ta gabata, kuma ya samu halartar wakilan sama da 1500 daga kasashen Afrika dama sauran sassan duniya.

Taken taron na bana shi ne, 'ci gaban Afrika: karuwa ko raguwa?', kwararru da dama sun halarci taron sun yi musayar bayanai game da ko kasashen na Afrika suna kokarin cike gibi da samar da damammaki domin samun makoma mai kyau a yankunan.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, tattalin arzikin Afrika yana habaka, lokaci ya yi a kara zuba jari a nahiyar. Ya kara da cewa, kasashen Afrika suna maraba da kamfanoni masu zaman kansu na gida da na kasashen ketare da su kara zuba jari domin habaka tattalin arzikin nahiyar, sannan ya ce, kasashen Afrika a shirye suke su samar da yanayi mai kyau na zuba jari.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China