in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin sun taimakawa matasan Afrika don cimma burinsu
2016-05-11 15:09:23 cri

Yanayin dunkulewar kasashen duniya baki daya, ya samar da dama ga matasan kasashen Afrika wajen cimma burin su. Alal misali kamfanonin kasar Sin da ke kasashen Afrika sun taimaka wa matasan Afrika da dama a wannan fanni.

An haifi matashiya Jalitti Ougiwa a karamin gari mai talauci da ke lardin Boothia dake kasar Kenya, matsalolin karancin abinci da yunwa, da cututtuka suna ciwo al'ummar wurin tuwo a kwarya.

Yayin da Ougiwa take karama, ta kan je aikin gona tare da mahaifiyarta, don samun kudade wajen ciyar da duk iyalinta mai kunshe da mutane 7. Ya zuwa yanzu, Ougiwa mai shekaru 21 ta cimma burin ta, ta zama kwararriya daya tak dake yankin yammacin kasar Kenya, da ta samu kyautar kudin karatu da gwamnatin Sin ke bayarwa, inda za ta je koyon digiri na biyu a jami'ar koyon ilmin sararin samaniyya ta Beijing.

Dalilin da ya sa ta samu cimma burin na ta, shi ne wani kamfanin kasar Sin da ya taimaka mata. Kamfanin kula da fasahar zirga-zirgar sararin samaniyya na Sin wato AVIC International ya shirya gasar fidda gwani game da sana'o'i karo na farko a nahiyar Afirka, inda Ougiwa ta yi fice cikin gasar, kuma ta samu damar karatu a birnin Beijing. Yayin da aka tabo maganar gasar, ta yi dariya tana mai cewa, a wannan yanki na karkara, ban taba zaton zan iya dogara ga karfina don samun damar karatu a kasar Sin ba.

Mahaifin Ougiwa Oumubo ya jinjinawa kamfanin Sin sosai. Ya ce, tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, Sinawa sun gina babban filin motsa jiki na Moi, kuma abun da ya kawo fasahohi da kwararru ga kasar Kenya. Yanzu, Sin ta sake ba da gudummawa ga diyar ta, don cimma burin.

Ougiwa ya bude wata taga ga mazaunan wurin, labarunta sun karfafa zukatan matasan Kenya, domin sun fahimta cewa, idan aka samu ilmi da fasaha, za a canja rayuwarsu.

Haka kuma, matashin Habasha Tadiyosi mai shekaru 29 shi ma ya ganewa idanunsa manyan ayyuka na kasar Sin. Ko da yake, matsahi ne amma ya zama babban injiniya a fannin fasalin hanyoyi, kuma jami'in kula da gine-gine na sashen hukumar kula da gine-ginen hanyoyi ta farko, a kamfanin CCCC a birnin Addis Ababa. Yayin da aka tabo rayuwar wannan matashi dan kasar Habasha, za a fahimci kokarin kamfanin kasar Sin.

Bayan da Tadiyosi ya samu wannan aiki, bai saba da al'adun kamfanin da mutanensu ba, kuma yana ganin cewa Sinawa suna da kokarin aiki, kuma ba su son jin dadin rayuwa. Amma bayan da ya kara fahimtar kamfanin, dabarun samun bunkasuwa na kamfanin ya burge shi, kuma ya karfafa masa gwiwa, kuma halin zumunci da kokarin aiki na Sinawa ya burge shi sosai.

A karkashin wannan yanayi, Tadiyosi ya daukaka, har ma kamfanin ya mika wasu muhimman ayyuka gare shi. A shekarar 2010, sashen hukumar kamfanin CCCC dake yankin gabashin Afrika ya dauki nauyin yin gyare-gyaren hanyoyi na babban filin jiragen sama dake Bole dake birnin Addis Ababa. Tadiyosi ya shugabanci wata tawagar, kuma sun kwashe watanni 3 don zayyana takardun gine-gine na wannan aiki.

Tadiyosi shi ma yana fata zai yada al'adun kamfanin Sin zuwa sauran wurare, ya ce, a cikin shekaru 6 da suka gabata, ya yi aiki da karatu tare da abokan aikin sa Sinawa, abun da ya fi burge shi shi ne, Sinawa suna da kokarin aiki da hazaka, kuma sun kware wajen gudanar da aiki cikin hanzari, kuma yana ganin cewa, wannan shi ne babban dalilin da ya sa Sin samun babban ci gaba a yanzu.

Ban da wannan kuma, wata dalibar kasar Uganda ta gode ma kasar Sin bisa damar da Sin ta ba ta wajen aiki. A shekarar 2012, Lailla ta kammala karatun kasuwanci a wata jami'ar dake kasar Uganda, ta yi fama da matsalar rashin aikin yi, sabo da a ko wace shekara, a kasar Uganda, akwai dalibai kimanin dubu 40 da suke kammala karatu, amma 8000 kacal ne ke samun gurbin aikin yi.

Abun farin ciki ne, bisa taimako daga wani jami'in hukumar kula da hanyoyi na kasar Uganda, Lailla ta samu damar shiga cikin kamfanin CCCC na kasar Sin, kuma ta zama jami'a a sashen kula da daukar sabbin mutane na kamfanin. Lailla ta ce, game da wannan aiki, kamfanin bai bukaci ma'aikata wadanda suka kware wajen aiki ba, kuma hakan ya ba da wata damar samun aikin yi. Ta gode wa wannan kamfani wanda ya ba ta dama ta samun aikin yi.

Laila tana alfahari da aikin ta a kamfanin. Ta gaya wa wakilinmu cewa, kamfanin CCCC ya samar da guraben aikin yi da yawansu kai sama da 3800, kuma sun horar da kwararru a fannin hanyoyin mota da gadoji da sauransu. Haka kuma, ta gaya wa wakilinmu cewa, kamfanin CCCC ya ba da babbar gudummawa game da raya muhimman ababen more rayuwa a kasar Uganda, ya samar da guraben aikin yi ga dubban al'ummar kasar Uganda, sabo da haka, wannan kamfani ya yi tasiri sosai a wurin.

Yayin da wakilinmu ya hadu da Laila a kwanan baya, ta samu lambar yabo ta kwarewa cikin fasahar fidda ma'aikatan Afrika da suka yi fice cikin kamfanonin Sin a kasar Uganda a karo na farko. Idan aka kwatanta da a baya, wato yayin da take damuwa game da neman aiki, yanzu, Lailla tana da kwarewa tana cikin murmushi. Ta kuma bayyana cewa, aiki a kamfanin kasar Sin ya ba da wani babban darasi gare ta, kuma ta karu sosai. Ta gode wa kamfanin kasar Sin, kuma ta gane ma idanun ta ci gaban da ta samu, abun da ya karfafa zukatanta, don ta kara kokari wajen cimma burinta. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China