Hare-haren da aka kai a yankin gabashin kasar Kongo(Kinshasa) sun haddasa mutuwar mutane 17
Kakakin sojojin gwamnatin Kongo(kinshasa) Mac Azukayi ya bayyana cewa, wasu dakaru dauke da makamai sun kai hare-hare kan kauyuka guda 2 da ke lardin Arewacin Kivu a yankin gabashin kasar Kongo(kinshasa) a ranar Talata da dare, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 17.
Mazauna wurin suna ganin cewa, dakarun ADF dake adawa da gwamnatin Uganda ne suka kai wadannan hare-hare.
Yankin gabashin kasar Kongo(kinshasa) dai yana makwabtaka da kasar Uganda. Dakarun ADF sun dade suna zaune a cikin kasar Kongo(kinshasa), kuma su kan kai hare-hare kan sojojin gwamnatin da jama'a.(Bako)