in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya umarci manyan hafsoshin tsaron da su kawo karshen hare-haren da ke faruwa a kasar
2016-04-28 20:35:41 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umarci babban hafsan tsaron kasar Janar Abayomi Olonisakin da babban sifeton 'yan sanda na kasar Solomon Arase da su ceto al'ummomin da ke fuskantar hare-hare da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa.

Shugaba Buhari ya bayar da wannan umurni ne jiya Laraba a Abuja, babban birnin kasar yayin bikin kaddamar da wani littafi, inda ya umarci jami'an tsaron biyu da su kawo karshen dukkan kungiyoyin da ke yiwa jama'a barazana a kasar.

Ya kuma bayyana kudurin gwamnatinsa na magance wannan matsala, yana mai cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunci irin wadannan hare-hare su ci gaba da faruwa ba.

Don haka ya kabulanci daukacin 'yan Najeriya, da su kasance masu kaunar kasarsu, ta hanyar rashin nuna bambancin kabila,addini da kuma ra'ayin siyasa, sannan su jingine duk wani ra'ayi kan marudun kasa.

A ranar 5 ga watan Maris ne wasu da ake zaton Fulani makiyaye ne suka kona wasu al'ummomi 7 kurmus a yankin Agatu dake arewa maso tsakiyar jihar Benue tare da kashe wasu daruruwa.

Sai dai wasu makiyayan da suka zanta da manema labarai, sun bayyana cewa, rikicin ya barke ne bayan da wasu 'yan kabilar ta Agatu suka kashe musu dabbobinsu kimanin 10,000.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China