in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Sin za ta kara samar da fa'idoji, in ji wani kwararre
2016-04-28 20:23:14 cri
Babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya Bola Akinterinwa ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Najeriya da Sin za ta kara samar da fa'idoji ga sassan biyu.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayin taron kasashen Sin da Afirka da ya gudana jiya Laraba a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Ya ce kokarin da gwamnati mai ci a Najerya ke yi na farfado da yarjeniyoyin da ke tsakanin sassan biyu da kara kulla wasu sabbi, ya sanya manufofin kasashen waje na kasar aza kasar Sin a muhimmin matsayi.

Ya kara da cewa, karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Sin, za ta inganta harkokin masana'antu a Najeriya, matakin da a cewarsa zai baiwa masu sha'awar zuba jari a bangaren masana'antu damar cimma bukantunsu sakamakon bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China