160428-akwai-makoma-mai-haske-bako.m4a
|
Yayin da jakadiyar Sin a kasar Ghana Madam Sun Baohong ke zantawa da wakilinmu, ta ce, akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwar tsakanin kasashen Sin da Ghana. Sun Baohong ta ce, Ghana ta zama daya daga cikin kasashen da ke kudu da Hamadar Sahara da suka fara kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin. Ta ce cikin tsawon lokaci, kasashen Sin da Ghana sun yi mu'amala tsakanin manyan jami'an su, kuma an samu sakamako mai gamsarwa wajen hadin gwiwar moriyar juna, da kara mu'amalar al'adu, da karfafa zumunci na gargajiya a tsakaninsu.
A shekarar 2015, a yayin taron kolin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wanda ya gudana a Johannesburg, shugabannin kasashen Sin da Ghana sun cimma matsaya guda game da karfafa dankon zumunci, da yalwata hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu.
Madam Sun Baohong ta ce, taron koli na Johannesburg ya tsara shirin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Afrika da yalwata hakikanin hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika daga duk fannoni, kuma hakan ya kara cusa sabbin abubuwa wajen raya dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Ghana daga duk fannoni, matakin da zai zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu daga duk fannoni.
Sun Baohong ta kara da cewa, "Kasar Ghana ta kafa rukunin aiki don cika alkawarin da aka dauka a yayin taron koli, kuma an kafa tsarin mu'amala tsakanin rukunin da ofishin jakadancin Sin da ke kasar Ghana, ana fatan sakamakon da aka samu a yayin taron koli zai kawo moriya ga kasar Ghana da jama'arta. Bangarorin biyu sun kuma tuntube juna don daukar matakan gudanar da hadin gwiwa a kasar Ghana, don cimma matsaya guda a fannoni da dama.
A cewar Sun Baohong, yanzu haka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Ghana ya kasance a sahun gaba wajen hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta fannoni daban daban, kuma Sin ta kasance daya daga cikin kasashen dake yawan yin cinikayya da kasar Ghana. A shekarar 2015, jimillar cinikin bangarorin biyu ta kai dalar Amurka biliyan 6.604, adadin da ya karu da kashi 18.2 cikin 100 bisa na shekarar da ta gabata. Har wa yau jarin da Sin ta saka a kasar Ghana kai tsaye kuma wanda ba na hada-hadar kudi ba, ya kai dalar Amurka miliyan 174, yayin da kuma kamfanonin Sin suka daddale kwagila game da gine-gine a kasar Ghana da kudin su ya kai dalar Amurka biliyan 1.286, masana'antu sarrafa iskar gas na Atuabo da tashar samar da ruwa ta Bui, haka ma a fannin da aikin samar da ruwa na Kaipeng, duk manyan ayyukan dake shafar tattalin arziki da zaman rayuwar al'ummar kasar, da kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gudanar da su, gami da tattara kudaden aiwatar da su.
Sun Baohong ta ce, kamfanonin Sin suna dora muhimmanci sosai game da kasuwannin kasar Ghana, kuma za su tashi tsaye game da raya ababen more rayuwa, da makamashi, da kirkire-kirkire, da aikin gona, da zirga-zirgar sararin samaniyya, da kadarorin gidaje da sauransu. Ban da wannan kuma, Sin ta saka jari ga kafa kamfanonin wutar lantarki da zirga-zirgar jiragen sama, matakin da ya taka muhimmiyar rawa wajen warware matsalar karancin wutar lantarki, da kara zirga-zirga a shiyya-shiyya. A daya hannun masana'antun Sin sun sauke nauyin dake kansu wajen bautawa al'ummar kasar Ghana, da kyautata masana'antu a wurin, kana sun ba da gudummawa wajen raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar al'umma a kasar.
Madam Sun ta ce. Abun da ya kamata a lura da shi, a cikin 'yan shekarun nan, an hada fasahohi, da kayayyakin kasar Sin, da masana'antu da jari na kasar Ghana, matakin da ya kawo wasu kyawawan masana'antu a kasar, kuma abun da ya kara gogayyar kasar Ghana wajen kera jiragen ruwa, da kiyaye muhalli, da kera motoci, hakan kuma ya kawo alheri ga zamantakewar al'ummar Ghana.
Sun Baohong ta ce, yanzu, Ghana na kokarin neman canja salon bunkasuwar tattalin arziki, da cimma burin raya masana'antu, don raya tattalin arziki da fitar da kayayyakin kasar zuwa ketare. Kasar Ghana na bukatar jari da fasahohi na kasar Sin, da koyon fasahohin samun bunkasuwar kasar Sin, da more sakamakon da Sin ta samu wajen raya kasa, da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Ghana. Kuma akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwa a fannin aikin gona, da samar da ababen more rayuwa, da zirga-zirgar sararin samaniyya, da makamashi, da tattara kudade don saka jari da hadin gwiwa wajen makamashi a tsakaninsu.
Madam Sun ta ce, makasudin ziyarar shugaban CPPCC Yu Zhengsheng a kasar Ghana shi ne inganta dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, da fadada mu'amala da hadin gwiwa, da samun amincewar juna tsakanin bangarori daban daban, kana da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da cimma matsaya guda tsakanin Sin da Ghana, wajen daukar matakai don cimma burin da aka tsara a yayin taron FOCAC na Johannesburg. Kana zai gabatar da sabuwar manufar Sin da ra'ayin kasar wajen hadin gwiwa da kasashen Afrika. Wannan ziyara ta nuna sahihiyar zuciyar kasar Sin wajen inganta hadin gwiwa ta sada zumunta da kasar Ghana.
Sun ta ce, ta wannan ziyarar Mista Yu Zhengsheng a kasar Ghana, za a kara raya dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu. (Bako)