160422-Hausawa-a-kasar-Sin-cinikayya-a-kasar-Sin-lubabatu.m4a
|
Hausawa kan ce, kasar Sin bangon duniya ce. Duk da haka, yayin ci gaban huldar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a shekaru 45 da suka wuce, al'ummar kasashen biyu na kara mu'amala da juna ta fannoni daban daban, kuma karin Hausawa na zuwa kasar Sin tare da wasu bururuka nasu. A gyara zama a saurari shirin dangane da rayuwar wasu Hausawa a kasar Sin, kuma a wannan mako za mu kawo muku labaran wasu 'yan kasuwa da ke gudanar da harkokin cinikayya a nan kasar.(Lubabatu)