Zhang Jianwei ya ce, kasar Sin da kasashen Larabawa na da dankon zumunci a tsakaninsu, kuma jam'iyyun Sin da kasashen Larabawa sun kara inganta mu'amala a tsakaninsu. A farkon wannan shekara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci yankin Gabas ta tsakiya, inda ya yi muhimmin jawabi a cibiyar kawacen kasashen Larabawa, ya nuna cewa, kasar Sin tana maraba da shugabannin kasashen Larabawa don su kai ziyara a kasar Sin, wannan taron da za a shirya ya zama matakin da aka dauka don gudanar da sakamakon da ziyarar shugaban Xi ya cimma.
A ranar 21 ga wata, za a kaddamar da taron a birnin Yinchuan, wakilai za su tattauna batutuwan "Zabin hanyar samun bunkasuwa", da tabbatar da zaaman lafiya da karko, da dangantakar dake tsakanin Ziri Daya da Hanya Daya, da jami'yyun gida da waje.(Bako)