160420-ziyarar-buhari-ta-samu-samako-gamsarwa.m4a
|
A makon da ya gabata, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki ta tsawon kwanaki 6 a kasar Sin, inda kasashen Sin da Nijeriya suka kara inganta hadin gwiwarsu a fannin wutar lantarki, da ma'adanai, da aikin gona, da dai sauransu. Sashen hausa na gidan rediyon CRI ya tura wakilai Samuni Alhassan da Aminu Xu don hada rahotanni, inda suka zantawa da gwamnoni da ministoci da 'yan kasuwa har da mai girma shugaban Buhari, sun bayyana cewa, lokaci ya yi da Sin da Nijeriya su inganta hadin gwiwa tsakaninsu, Nijeriya za ta ci gajiya daga cikin wannan hadin gwiwa.