in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jagoranci taron tattaunawa game da tsaron shafin Internet da harkokin sadarwa a kasar
2016-04-20 14:02:20 cri

A ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin kuma shugaban rukunin kula da tsaron yanar gizo da harkokin sadarwar kasar Xi Jinping, ya shugabanci taron tattaunawa game da tsaron yanar gizo wato internet da harkokin sadarwa a kasar, tare da yin jawabi, inda ya jaddada cewa, ya kamata a bi manufar kirkire-kirkire da daidaitawa da kiyaye muhalli, da bude kofa da more fasahohin da aka samu wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin, wannan ya zama babban sharadi wajen raya kasar Sin a yanzu da nan gaba, ya kamata sha'anin raya harkokin sadarwa da yanar gizo shi ma ya bi wannan ka'ida. Shugaba Xi Jinping ya ce, ya kamata a kokarta wajen raya kasar Sin a fannin shafin Internet, don kawo moriya ga kasar da jama'arta.

Da safiyar ranar 19 ga wata, shugaban kamfanin Alibaba Ma Yun da shugaban kamfanin Huawei Ren Zhengfei sun zauna kusa da shugabannin kasar ta Sin Xi Jinping, Li Keqiang da Liu Yunshan, inda suka ba da wasu shawarwari game da tabbatar da tsaron shafin Internet da raya harkokin sadarwa a kasar. Haka kuma, wasu shahararrun kwararru da masana a fannin shafin Internet da harkokin sadarwa, kana da wasu jami'an da ke kula da yada labaru na kasar sun halarci taron.

A yayin taron, shugaban Xi ya tabo maganar tunanin raya sha'anin harkokin sadarwa da shafukan Internet, da matakan da za a dauka don samu fasahohin zamani a fannin, ya ce,"A kasar Sin akwai masu amfani da shafin Internet da yawansu ya kai miliyan 700, kuma wannan ya zama wani babban ci gaba da Sin ta samu. Bayan da Sin ta shiga wani sabon matakin raya tattalin arziki, ya kamata a kara cusa sabbin abubuwa wajen sa kaimi ga tattalin arziki, game da wannan, ya kamata a yi amfani da shafin Internet don cimma wannan buri. Haka kuma, idan ana son samun cigaba a wannan fanni, dole ne a bi manufar raya wannan sha'ani don jama'a."

Shugaba Xi ya ce, ya kamata a gaggauta nazarin hidimomin sadarwa da aka bayar, don rage farashin yin amfani da shafin Internet, don kara sanya miliyoyin mutane su samu damar more ci gaban da harkokin shafukan Internet ke kawo. Sa'an nan, bayan da jama'a suka kara duba shafukan Internet, za su iya bayyana ra'ayoyi a Internet, shi ya sa ya kamata shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na matakai daban daban su samu fahimtar tunanin jama'a ta shafukan Internet. Ya ce, "Duk masu duba shafukan Internet jama'a ne, ya kamata a nuna hakuri game da wadannan mutane, idan suka ba da shawarwari masu kyau, ya kamata a bi su, idan suka gamu da wahalhalu, dole ne a taimaka musu. Idan ba su fahimci wani abu ba, dole ne a fadakar da su. Idan suka samu rashin jin dadi, ya zama wajibi a warware batun, idan suna da kuskuren tunani, dole ne a canja shi."

Ya jaddada cewa, dole ne a samar da shafukan Internet masu kyau ga masu duba shafukan Internet, musamman ma matasa, dole ne a dauki matakai bisa la'akari da ra'ayoyin jama'a wajen kyautata shafukan Internet.

A yayin wannan taron, Xi Jinping ya ce, ya kamata a kara ware kudade, da daukar kwararru, da ba da kayayyaki don tabbatar da nazarin kan wannan batu. Ya ce, sabbin fasahohi sakamako ne na ci gaban wayin kan dan, duk abin da zai kawo karuwar GDP da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma, Sin ba za ta ki su ba.

Game da bunkasuwar da wasu kamfanoni a fannin shafukan Internet suka samu, Xi Jinping ya nuna yabo kuma ya ce, ya zama wajibi a sa kaimi da nuna goyon baya ga kamfanoni da su kirkiro sabbin tunani, da nazarin sabbin fasahohi, don kara takara da sauran kamfanoni na kasashen duniya. A sa'i daya kuma ya jaddada cewa, kasar Sin tana maraba da kamfanonin shafukan internet da suke bi dokokin Sin don su bude harkokinsu a nan. Ya ce, "Kofofin Sin a bude suke, ba za ta rufe su ba. Kamfanonin shafukan Internet na kasashen waje, idan suka bi dokokin kasar Sin, za a yi maraba da su."

Shugaban Xi ya ce, bunkasuwar harkokin sadarwa da shafukan Internet na Sin ba ta iya rabuwa da kwararru, ya ce, "Ya kamata a canja tunani don daukar kwararru da kaunarsu, da tsara manufofi na musamman gare su, kana ya kamata a kafa wani tsarin sa kaimi ga raya kwararru don su kara ba da gudummawa ga kasar Sin."(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China