in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban Sin ya halarci bikin kama aikin shugaban Kongo(Brazzaville)
2016-04-18 11:32:23 cri
A ranar 17 ga wata, shugaban kasar Kongo(Brazzaville) Denis Sassou-Nguesso ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Sin wato ministan kula da harkokin gidaje da raya birane da garurruwa na kasar Chen Zhenggao.

A yayin ganawar Chen Zhegngao ya mika kyakkyawar gaisuwa ta shugaba Xi ga takwaransa Sassou. Ya ce, kasashen Sin da Kongo(Brazzaville) kyawawan abokai kuma aminai ne, kuma sun samu sakamako mai kyau kan hadin gwiwar dake tsakaninsu daga duk fannoni. Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Kongo(Brazzaville), don yalwata dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa daga duk fannoni a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. Kasar Sin tana nuna goyon baya ga jama'ar Kongo(Brazzaville) da su lalubo hanyar samun bunkasuwa da ta dace da yanayin kasar, kuma ya yi imani cewa, a karkashin shugabancin Sassou, kasar za ta kara samun babban ci gaba.

A nasa bangare kuma, shugaba Sassou ya yaba wa shugaba Xi da ya tura manzon musamman don halartar bikin kaman aikinsa, kuma ya isar da gaisuwa da godiya ga takwaransa na Sin Xi Jinping.

Mista Sassou ya ce, bayan da Kongo(Brazzaville) da Sin suka kafa dangantakar diplomasiyya a tsawon shekaru 52, dangantakar kasashen biyu ta samu habaka, duk da canjin yanayin kasa da kasa. Kasar Kongo(Brazzaville) tana fatan hadin gwiwa da kasar Sin kafada da kafada don tinkarar kalubale da samun ci gaba tare yayin da take kokarin raya masana'antu da zamanintar da kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China