in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahohin aikin gona lardin Gansu na Sin yana taimakawa kasashen Afrika
2016-05-03 07:20:39 cri

Yayin da kwararren malami a fannin aikin gona na cibiyar nazarin kimiyyar da ta shafi halittu na jami'ar Lanzhou Li Fengmin ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, ya kamata a raya fasahar aikin gona da aka samu a lardin Gansu wadda ta dace da yanayin karancin ruwa, don kawo moriya ga jama'ar lardin, har ma sanya jama'ar kasashe masu tasowa daban daban su ma su ci gajiya aikin.

Daga shekarar 2010, a karkashin aikin hadin gwiwa da raya fasahar aikin noman rani a kasashen Afrika da Sin da M.D.D. da ma'aikatar kula da kimiyya da fasahar kasar Sin ta shirya, Li fengmin ya shugabanci tawagar nazarin halittun da suka iya rayuwa a cikin yanayi maras isasshen ruwa na jami'ar Lanzhou, don gudanar da wannan aiki na lalubo bakin zaren warware matsalar fari a kasashen Afrika, kana da fasahar tsimin ruwa don kyautata fasahar aikin gona.

Li Fengmin ya ce, an samu babban ci gaba game da fasahar kara amfanin gona ta hanyar da suka kirkiro a lardin Gansu, kuma wannan yana da ma'anar musamman ga kasashen Afrika. Suna fatan yin amfani da gwaje-gwaje don neman hanyar da za a bi wajen warware matsalar fari da nazarin fasahar tsimin ruwa don habaka aikin gona, kuma za su yi amfani da kafa misali da yalwata fasahohi, don kara yawan amfanin gona a kasashen Afrika, ta hakan ne za a cimma burin samar da wadataccen abinci a kasashen Afrika.

Mista Li ya fada wa wakilinmu dalilin da ya sa ya samu kwarin gwiwa. Ya ce, Lardin Gansu ya yi fice wajen raya aikin gona a lokacin Rani a kasar Sin gaba daya, kuma matsalar fari da take daibaibaye lardin da yanayin raya tattalin arziki da zamantakewar wurin sun yi daidai da hali na wasu kasashen Afrika. Fasahohin da suka samu wajen habaka aikin gona a lokacin Rani ya fi dacewa da nahiyar Afrika, sabo da haka, lardin Gansu yana da fifiko wajen inganta hadin gwiwar nazari da kasashen Afrika game da raya aikin gona a lokacin Rani.

Li Fengmin ya kara da cewa, kasashen Afrika da dama kamar Kenya ba su da karfi wajen tinkarar matsalar fari, musamman ma a shekarar 2011, Kenya ta gamu da matsalar fari da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 60 da suka gabata, sana'o'in shuke-shuke da kiwon dabbobi sun fuskanci babbar hasara. Yanayi na lardin Gansu da na kasar Kenya sun yi kama da juna, amma akwai dan bambanci tsakaninsu, lardin Gansu yana yankin arewacin duniya, akwai yanayi 4 a wajen cikin shekara guda, yayin da kasar Kenya, tana kusa da Equator, kuma yanayin wurin na da dumi, sa'an nan yanayin kasa na wadannan kasashe 2 su ma, akwai bambanci, sabo da haka, bai kamata a yi amfani da fasahohin da lardin Gansu ya samu kai tsaye ba, dole ne a canja wasu abubuwa.

Li Fengmin da tawagarsa sun tashi tsaye don kyautata fasaharsu da kirkiro da sabbin tunani, don sanya fasaharsu ta dace da labarin kasa a nahiyar Afrika. Zuwa yanzu an samu shaidu da yawa da suka tabbatar da cewa, fasahohin da Sin ta samu na kara amfanin gona a lokacin Rani yana da saukin fahimta, kuma farashinsu yana da araha, abun da ya dace da yanayin da kasashen Afrika ke ciki.

A cikin shekaru da dama masu zuwa, Li Fengmin da tawagarsa zasu ziyarci kasashen Kenya da Habasha don kirkiro da sabbin fasahohi da kafa misali.

Ya zuwa yanzu, Li Fengmin da tawagarsa sun kafa yankunan gwaji da fadinsu ya kai murabba'in mita sama da 4000 a kasar Kenya, kana da tashoshin gwaji da fadinsa ya kai ekka sama da 100, ban da wannan kuma, sun yi amfani da fasahar zamani, don nazarin shuka masara da alkama da kafa misali wajen shuke-shuke, da horar da masu aikin gona da manoma a wuraren, da karfafa zukatansu wajen gudanar da gwaji a gonakinsu. Haka kuma, manoma da jami'ai a fannin aikin gona da ba su amince da wannan a lokacin da ya shude ba, yanzu, suna maraba da wannan sosai.

Ban da kasar Kenya, a karkashin shugabancin Li Fengmin, an yada fasahar aikin gona a lokacin Rani na lardin Gansu zuwa sauran kasashen Afrika ciki har da Habasha, da Zambiya, abun da ya sa aka horar da mutane masu aikin gona na kasashen Afrika da yawansu ya kai sama da dubu 10.

Li Fengmin ya ce, an yada fasahohin aikin gona a lokacin Rani da aka samu a yankin arewa masu yammacin kasar Sin zuwa yankuna masu fama da matsalar fari a kasashen Afrika, abun da zai kawo babban canji ga yawan amfanin gona da ake samu a kasashen Afrika.

A kasashen Kenya, da Habasha, bayan da aka yi amfani da gwajin, da kafa misali, da yalwata fasahohi, yawan amfanin gona da aka samu ya ninka sau 1, don haka akwai makoma mai haske game da wannan fanni.

Li Fengmin da tawagar nazarinsa sun bayyana cewa, bisa kidayar da suka yi, za a iya yin amfani da gonaki da fadinsu ya kai kashi 1 cikin 3 na fadi dukkan gonakin kasar Kenya, don samar da isassun abinci ga daukacin al'ummar kasar.(BAKO)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China