in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Sin
2016-04-17 12:11:14 cri

Najeriya ta kasance babbar aminiya ga kasar Sin, kuma dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Najeriya tana cigaba da samun bunkasuwa sannu a hankali, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu a ranar 10 ga Fabrairun shekarar 1971, wato a wannan shekarar ta 2016 dangantar dake tsakanin Sin da Najeriya ta cika shekaru 45 da kafuwa, a tsawon wadannan shekaru, an samu nasarori da cigaba mai tarin yawa a fannoni da dama, da suka hada da hadin gwiwa a fannin kasuwanci, da sadarwa, da tattalin arziki, da ilmi, da kiwon lafiya da raya al'adu da sauransu. Bisa wadannan tarin dalilai, shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cigaba da bunkasa wannan dadaddiyar alaka, hakan ne tasa ya yanke shawarar yin tattati zuwa kasar Sin domin ziyarar aiki har na tsawon kwanaki 5, kuma shugaban yana tare da babbar tawagar da suke masa rakiya, wadanda suka hada da wasu daga cikin ministocinsa, da gwamnonin jahohi, da sauran manyan jami'an gwamnati. Bisa ga tsarin wannan ziyara, shugaba Buhari zai gana da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping da wasu kusoshin gwamnatin kasar Sin, domin kulla yarjejeniya a fannoni dabam dabam da suka hada da aikin gona, da hakar ma'adanai, da huldar cinikayya, da bunkasa samar da kayayyaki, da ci gaban masana'antu, da zuba jari da samar da kayayyakin more rayuwa da dai sauran su.

Bugu da kari, shugaban Najeriyar zai ziyarci wasu daga cikin muhimman biranen kasuwanci na kasar Sin, da suka hada da Shanghai da Guangzhou. Akwai al'ummar Najeriya masu yawan gaske dake huldar kasuwanci da kasar Sin, da masu karatu a jami'oi da makarantun kasar, a fannonin ilmi dabam dabam, kuma cikin wadannan shekaru an samu gagarumin ci gaba a mu'amalar dake wanzuwa tsakanin al'ummomin kasashen biyu, wannan wata alama ce dake nuna cewa akwai babbar nasara game da hadin kai dake tsakanin kasashen biyu. (Ahmad Fagam, Saminu Alhassan, Mamane Ada, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China