Rahoton ya bayyana cewa, akwai damar samun bunkasuwar tattalin arziki na yankin gabashin Asiya da tekun Fasific, kuma an yi hasashe cewa, daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2018, saurin bunkasuwar da tattalin arzikin wannan yanki zai samu zai kama hanya yadda ya kamata. An kimanta cewa, yawan karuwar tattalin arziki na wannan yanki zai kai kashi 6.3 cikin 100 a shekarar 2016, kana gamayyar kasashen wannan yanki ban da kasar Sin za ta samu saurin karuwar tattalin arziki da yawansa zai kai kashi 4.8 cikin 100, kuma abun da zai fi saurin karuwar da aka samu a shekarar bara, amma akwai bambanci game da makomar raya tattalin arziki na yankunan daban daban.
Bankin duniya ya ce, ya zama dole gamayyar tattalin arziki daban daban su mayar da manufar kudi a gaban kome, kana da yin gyare-gyare game da tsarinsu. Bankin duniya ya yi kira ga gamayyar tattalin arziki daban daban da su yi tsanaki wajen aiwatar da manufofin kudi da tinkarar hadarurruka da za a samu, kana gwamnatocin kasashe daban daban su rage shingayen da suka kafa game da yin ciniki a shiyya-shiyya. (Bako)