A cikin sakon, firaministan Li ya ce, raya kimiyya da fasaha a fannin nukiliya ya zama muhimmin ci gaba da dan Adam ya samu a karni na 20. Ya ce amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da samun isassun makamashi, da sa kaimi ga raya tattalin arziki, da warware batun sauyin yanayi, da kawo alheri ga jama'a da dai sauransu.
Li Keqiang ya kara da cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya makamashin nukiliya, da nace kan amfani da nukiliya don samar da wutar lantarki yadda ya kamata. Kana ta kafa tsarin raya masana'antu ta fasahar makamashi, za kuma ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya wajen amfani da makamashin nukiliya ta hanyar lumana, a karkashin inuwar zaman tare, da hadin gwiwa don samun nasara tare. (Bako)