in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rattabata hannun kan yarjejeiya tsakanin kasar Sin da Najeriya ta harba tauraro dan adam
2016-04-13 09:33:08 cri
A yau Litinin ne kamfanin China Aerospace Science and Technology Corporation(CASC), da kamfanin sadarwa na Najeriya NIGCOMSAT LTD, suka rattaba hannu don kulla yarjejeniyar samarwa tare da harba tauraron dan adam na biyu 2 da na 3, wato NigComSat 2 and 3 zuwa sararin samaniya.

Da yake zantawa da wakilin sashen Hausa na gidan radiyon kasar Sin CRI a harabar kamfanin CGWIC dake birnin Beijing, ministan ma'aikatar sadarwa ta Najeriya Barista Abdur-Rahim Adebayo Shittu, ya bayyana cewar aikin samar da tauraron dan adam na 2 da na 3 zai bunkasa fannin kimiyya da fasahar sadarwa ga Najeriya, sannan ya bayyana cewar gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniyar diplomasiyya da kasar Sin, sama da shekaru 45 da suka gabata.

Barrista Shittu, ya bayyana cewar Najeriya na da kyakkyawar mu'amala ba ma da gwamnatin kasar Sin kawai ba, har ma da kamfannonin kasar Sin, sakamakon kyakkyawar fahimta dake tsakanin kasashen biyu, da mutunta juna, da cin moriya a fannonin da suka shafi sadarwar, da kiwon lafiya da harkokin gwamnati ta hanyar amfani da fasahar zamani da dai sauransu.

Ministan ya bayyana cewar aikin samar da tauraron dan adama na 2 da na 3 zai taimakawa Najeriyar ta fuskar samar da ayyukan yi da ci gaban tattalin arziki da tsaro da dai sauransu.

Bugu da kari Ministan ya bayyana cewar Najeriya ta gayyaci kamfanonin kasar Sin da su samar da fasahohin zamani na wayar salula a kasar domin samun karin ci gaba.

Da yake bayani game da kulla yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu, Shugaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya Muhammad Ogoshi daga jihar Nasarawa, ya bayyana cewar aikin zai taimakawa wajen raya tattalin arzikin Najeriya daga bangarori daban daban, domin yanzu a duniyarmu kusan babu wani aikin da ba ya bukatar na'urori iri na zamani.

Ogoshi ya ce, dukkan ayyukan da suka shafi kiwon lafiya, noma, da gine gine, da neman aikin yi dukkan su suna bukatar fasahar sadarwa ta zamani.

Sannan ya ce, kulla yarjejeniyar ya kasance a matsayin shimfida ga ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kawo nan kasar Sin.

Game da huldar dake tsakanin kasar Sin da ta Najeriya kuwa, dan majalisar ya ce kasar Sin kasa ce mai karfi wadda kusan dukkan al'amuran da ake gudanar a duniya ba za a rasa wasu bangarorin da suka shafi kasar Sin ba. (Ahmad/Bello)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China