in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya a ganin wani dan kasar Sin da ke zaune Kenya
2016-04-06 12:18:26 cri

An haifi Han Jun shekarun 50 na karnin da ya wuce a birnin Huai Nan dake lardin Anhui na kasar Sin. A shekarar 1992, ya bar aikinsa a matsayin shugaban wani kamfani na kasar Sin, don kai ziyara a kasar Kenya dake yankin gabashin nahiyar Afrika, tare da fatan samun aiki mai kyau a wurin, bayan shekaru sama da 20, musamman ma a cikin wadannan shekaru, Han Jun ya gane wa idanunsa kyautatuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Kenya.

Han Jun ya ce, bayan da aka gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, Sinawa da dama sun bar kasar su,don gudanar da aiki a kasashen waje, musamman a fannonin aski, da dinki ko dafa abinci.

A farkon shekaru 90 na karnin da ya wuce, Sinawa da ke kasar Kenya ba su da yawa, yawan Sinawa dake kasar ya kai kimanin 200, yayin da wasu daga cikinsu suna dogaro kan aikin dafa abinci da sauransu. A lokacin, yawan gidajen cin abinci na kasar Sin a kasar Kenya bai kai 10 ba, kuma akwai wani gidan cin abinci mai suna "Chinese Plate", amma shugaban gidan cin abinci wani dan kasar India ne, sai dai akwai wasu kuku Sinawa dake aiki a wurin, an lakaba masa wannan suna saboda su. Daga bisani kuma, wasu daga cikin kuku-kukun sun bude gidajen cin abinci na kansu, kuma sana'o'i su sun samu ci gaba. Yanzu, yawan gidajen cin abinci na Sinawa a birnin Nairobi kawai ya kai 80.

Han Jun ya kara da cewa, a lokacin, Sinawa a kasar Kenya suna zuwa neman arziki ne. A shekaru 90 na karnin da ya wuce, yawan masana'antun kasar Sin a kasar Kenya bai da yawa, akwai wasu masana'antun gwamnati dake gudanar da aikin ba da tallafi a wurin, kuma sun ba da agaji ga wasu manyan ayyuka a wurin.

A wancan lokacin, kasar Kenya da sauran kasashen yammacin duniya su na tuntubi juna sosai, amma ba ta hulda da Sin sosai. A lokacin, yayin da akasarin jama'ar kasar Kenya suka ambaci Sin, suna ganin cewa, Sin wani yanki ne da ke da talauci, ko koma bayan tattalin arziki, kuma suna zaton cewa, a kasar Sin namiji guda zai iya auren mata da yawa, kuma jama'ar kasar Sin suna zaman kashe wando.

A karni na 21, kenya ta canja manufar diplomasiyya inda ta fara mai da hankali kan kasashen da ke gabashin duniya, kuma ta kara karfafa huldar dake tsakaninta da kasar Sin. A karshen shekarun 90 na karnin da ya wuce, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya ta samu kyautatuwa, wanda hakan ya kara sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayyar bangarorin biyu.

A farkon karni na 21, kamfanonin Sin da dama sun fara shiga kasar Kenya, kuma Sinawa sun fara gudanar da aikin gine-gine da saka jari a kasar. Bisa labarin da aka samu, an ce, kamfanonin Sin sun gudanar da manyan ayyukan gine-ginen da yawansu ya kai rabin jimillar wanda aka gudanar a kasar.

Kamfanonin Sin sun dauki nauyin shimfida hanyoyin jiragen kasa a ketaren yammaci da gabashin kasar, da tsawonsa ya kai sama da kilomita 400, wanda ya hada birnin Mombassa wato birnin dake gabar teku da Nairobi hedkwatar kasar tare. Jimillar kwangilar shimfida hanyoyin jiragen kasa ta kai dalar Amurka biliyan 4, kuma bankin kula da shige da ficin kayayyaki na Sin Exim Bank, ya ba da kudin rance da yawansu ya kai kashi 90 cikin 100 na wannan kwagila. Bayan da aka kammala aiki, za a rage lokacin tafiya daga Mombasa zuwa Nairobi zuwa awoyi 4.5, a maimakon awoyi 10 da ake yi yanzu. Aikin gina wannan hanyar jiragen kasa ta kasance mataki na farko cikin ayyukan da kasar Sin za ta yi wajen taimakawa kasashen Kenya, Uganda, Rwanda, da Tanzaniya, wajen kafa hanyoyin jiragen kasa da ke hada kasashen yankin Gabashin Afrika baki daya tare.

Ban da wannan kuma, a cikin 'yan shekarun nan, cinikin dake tsakanin kasashen Sin da Kenya ya habaka sosai.

A shekarun 90 na karnin da ya wuce, yayin da Han Jun ya ziyarci kasar Kenya a karon farko, ya bude wani shagon sayar da kayayyakin sassaka na kasar Sin. Ya ce, a lokacin, dalilin da ya sa ake fitar da kayayyaki zuwa kasashen Afrika, sabo da ana kera kayayyaki fiye da kima a kasar Sin, kuma kasashen Afrika ba su kasance manyan abokan ciniki na kasar Sin ba, akasarin abubuwan da Sin ta ke fitarwa zuwa kasashen Afrika kananan kayayyaki ne.

Ya kara da cewa, a lokacin, kasar Sin ta taba sayar da wasu manyan motoci ga kasar Kenya, amma sun kasance sau daya kawai, ba a ba da hidimmomi sosai ba, sabo da ba a bude kasuwanni yadda ya kamata ba. Han Jun ya ce, bayan da aka shafe shekaru kimanin 20, yanzu Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya ta kasar Kenya.

Daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba na shekarar 2015, yawan cinikin dake tsakanin kasashen Sin da Kenya ya zarce dalar Amurka biliyan 5, kuma abun da ya ci gaba da karuwa, saurin bunkasuwa da hakan ya samu ya kai kashi 20 cikin 100.

Yanzu, Kenya na shigar da manyan na'urorin kera kayayyaki daga kasar Sin, kamar na'urorin yin madubi, da yin dab'i da manyan na'urorin kera kayayyaki, da sauran kayayyakin kimiya da fasaha, haka kuma kamfanonin kasar Sin sun kara dora muhimmanci sosai game da hidimomin da za su bayar, kana farashin kayayyakinsu ya fi araha, idan aka kwatanta da takwarorinsu da aka yi a kasashen yammacin duniya.

A wata sabuwa kuma, Han Jun ya gane ma idanunsa babban canjin tunanin al'ummar kasar Kenya game da Basine. Yanzu, ba wani mutum da zai zaci kasar Sin wuri mai talauci, ko koma bayan tattalin arziki, Akasarin al'ummar Kenya na kallon kasar Sin a matsayin wadda ta samu babban ci gaba. Manyan kayayyakin da suke amfani da su, an shigo da su daga kasar Sin.

Bayan da danganatakar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya ta ci gaba da bunkasuwa, yanzu, yawan Sinawa da ke kasar Kenya ya ci gaba da karuwa. Bisa hasashen da aka yi, an ce, yawan Sinawa da suka samu lasisin zama a kasar Kenya ya kai fiye da dubu goma, sannan a ko wace shekara, yawan masu bude ido na kasar Sin da suka zuwa yawon shakatawa a kasar Kenya na karuwa zuwa sama da dubu 10, a maimakon 'yan dubbai a shekaru 90 na karnin da ya wuce.

Yanzu, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da hadin gwiwa a tsakaninsu, ta shiga wani sabon yanayi, musamman ma bayan da aka kafa dangantakar abokantaka irin ta hadin gwiwa da moriyar juna, da amincewar juna daga duk fannoni. Irin wannan hulda ta kasance wani misali ga kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, in ji Han Jun. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China