in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron tsaron Nukiliya karo na 4 a Washington
2016-04-07 09:14:41 cri

Taron tsaron nukiliya na bana zai ci gaba da kasancewa muhimmin dandali da kasashen duniya ke tattauna al'amura masu alaka da karfafa tsaron sinadarai da fasahohi tare da wuraren sarrafa ma'adanan Nukiliya kammar yadda al'adar taron ta kasance tun a baya.

A bana za a gudanar da wannan taro ne a birnin Washington na kasar Amurka tun daga ranar Alhamis 31 ga watan Maris, kuma ana sa ran shugabannin duniya da dama za su halarci taron. Baya ga mai masukin bakin taron wato shugaba Barck Obama na Amurka, an gayyaci kungiyoyin kasa da kasa 4, da shugabannin kasashen duniya sama da 50, ciki hadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da firaministan Birtaniya David Cameron, da na Canada Justin Trudeau, da shugaba Francois Hollande na Faransa, da firaministan India Narendra Modi, da dai sauransu.

Ko da yake cikin watan Oktoba na shekarar bara Rasha ta sanar da cewa ba za ta halarci taron ba, bisa zargin cewa Amurka na son maida batun tsaron Nukiya wani aikin kashin kai, wanda a hakikanin gaskiya a cewar Rasha aiki ne na kungiyoyin kasa da kasa. Rasha na ganin a maimakon halartar taron za ta maida hankali ga inganta alakarta da hukumar mai kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA a takaice.

Duk dai da wannan mahanga ta Rasha wadda ta sha banban da ra'yin sauran ragowar kasashen duniya, a hannu guda ana sa ran mahalarta taron a wannan karo za su tattauna game da matakan kaucewa fadawar makamai masu tsananin hadari hannun 'yan ta'adda.

Kaza lika nahiyar Asiya za ta taka muhimmiyar rawa a fagen cimma nasarar taron, musamman ma duba da yadda kasashen nahiyar masu yawa ke kokarin bunkasa amfaninsu da sinadaran nukiliya a ayyukan fararen hula, da kuma ci gaba da suke kara samu wajen raya fasahar Nukiliya.

A ranar Jumma'a 1 ga watan Afirilu shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron na bana game da matsayin kasar Sin a fannin tsaron Nukiliya. A daya bangaren batun matakan da suka dace a dauka kan Koriya ta Arewa, batu ne da mai yiwuwa ya zamo ciki na gaba gaba a wannan taro. Ana kuma sa ran shuwagabannin kasashen da wannan batu ya shafa za su gana gaba da gaba domin musayar ra'ayoyi kan batun, musamman ma shuwagabannin kasashen Amurka da Sin da Koriya ta kudu da firaministan Japan.

A daya bangaren akwai batun nukiliyar Iran wanda kasashe shida (Birtaniya, da Faransa, da Sin da Rasha da Jamus da Amurka) ke tattauna a kai. (Saminu Hassan, Mamane Ada, Ahmad Fagam, Sanusi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China