160401-Yankin-tattalin-arzikin-musamman-iri-na-Sin-a-Afrika-Lami.m4a
|
A wurin dake daba da birnin Lagos na kasar Najeriya, kamfannonin gine-gine na kasar Sin sun kafa wani yankin tattalin arziki na musamman domin jawo karin jarin kasashen waje. Kamar yadda birnin Shenzhen ya samu bunkasuwa bayan da ya zama yankin tattalin arziki na musamman na kasar Sin. A halin yanzu, birnin Shenzhen ya zama masana'antun duniya, kuma an fara gwajin aiki wajen kafa irin wannan yanki a kasashen Afrika.