in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmiyar Sanarwa!
2016-03-31 20:33:22 cri
A ci gaba da gabatar muku da kayatattun shirye-shirye masu ban sha'awa, sashen Hausa na Rediyon kasar Sin CRI, ya tsara wasu sabbin shirye shiryen bidiyo na harshen Hausa, wadanda gidan talabijin na tarayyar Najeriya NTA, zai nuna su ta kafar "Star Times".

Shirin DALIBAI A CHINA

Za a nuna shi a ranar Talata 12 ga watan Afirilu, da misalin karfe 7.30 na dare, a kuma maimaita ranar Laraba 13 ga watan na Afirilu, da misalin karfe 10 na safe.

Sai kuma shirin KASUWANCI A CHINA

Wanda za a nuna a ranar Laraba 13 ga watan Afirilu da karfe 7 na dare, a kuma maimaita shi a ranar Alhamis 14 ga watan na Afirilu, da karfe 10 na safe.

Akwai kuma shirin SOYAYYA A CHINA

Wanda za a nuna a ranar Alhamis 14 ga watan Afirilu, da misalin karfe 3 na yamma, a kuma maimaita ranar Jumma'a 15 ga watan Afirilu, da karfe 7 na safe

Da fatan mai sauraro zai kasance da NTA a kafar "Star Times" domin nishadantuwa da wadannan shirye shirye na CRI Hausa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China