in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu nasarar shirya babban zaben jamhuriyar Nijar
2016-03-31 15:06:54 cri

An gudanar da zagaye na farko na babban zaben jamhuriyar Nijar ne a ranar 21 ga watan Faburairun wannan shekarar, zaben da 'yan takara 15, wadanda babbar kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da takardunsu suka shiga. Kaza lika baya ga zaben shugaban kasa an kuma zabi wakilan majalissar dokokin kasar mai mambobi 171.

Daga cikin 'yan takarar kujerar shugabancin kasar akwai shugaba mai ciki yanzu Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS-TARAYYA mai mulki, sai kuma Seyni Oumarou na jam'iyyar MNSD-NASARA, da Hama Amadou na jam'iyyar LUMANA-AFRICA. Sauran 'yan takarar sun hada da Mahamane Ousamane na jam'iyyar ALHERI, da Abdou Labo na jam'iyyar CDS-RAHAMA da dai sauran su.

Tuni dai hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato CENI, ta bayyana sunan shugaba mai ci Mahamadou Issoufou, a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da aka kada zagaye na biyu na zaben a ranar 20 ga watan nan na Maris. Gabanin hakan dai shugaba Mahamadou Issoufou ya samu kaso kusan 48 bisa dari ne na kuri'un da aka kada, kasa da kaso 50 bisa dari da ake bukata domin lashe zaben.

A zagaye na biyu kuma, shugaban mai ci ya samu kusan kaso 92.5 bisa dari na jimillar kuri'un, bayan da dama daga sauran 'yan takarar suka soki sakamakon zagayen na farko. Kaza lika Hama Amadou na jam'iyyar LUMANA-AFRICA shi ke biye a matsayi na biyu a zaben na bana.

Masu sanya ido na kasa da kasa, da wakilan kungiyoyin nahiyar Afirka da dama sun bayyana gamsuwa game da sakamakon zaben, suna masu cewa zaben ya gudana lami lafiya, duk da jinkiri da aka samu wajen fara kada kuri'u a wasu sassan kasar.

Masharhanta dai na ganin akwai bukatar hukumar zaben kasar ta zage damtse, wajen shawo kan matsalolin da aka fuskanta a wannan karo, yayin zabukan kasar na gaba. Hakan kuwa na zuwa ne a gabar da wani sashen na 'yan adawar kasar ke ganin bai ma amince da sakamakon da aka fitar ba.

Duk da korafe-korafe da aka samu a lokaci da bayan kallamar zaben, masu sharhi na ganin gudanar da zabuka lami lafiya a kasashe da dama dake nahiyar Afirka, na alamta cewa hankulan al'ummun Afirka na kara karkata ga muhimmancin rungumar salon dimokaradiyya yadda ya kamata, da siyasa ba da gaba ba. A wani yanayi da ake ganin na iya bunkasa ci gaban nahiyar, wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana, tare da samar da dorewar salon mulki na dimokaradiyya. (Saminu Alhassan, Mamane Ada, Ahmad Fagam, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China