in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta nuna munafunci yayin da take musunta amfanin dokar yaki da ta'addanci ta Sin
2016-03-23 12:15:43 cri

A halin da ake ciki yanzu, ana fuskantar ayyukan ta'addanci a duk fadin duniya, haka ma a kasar Sin, a saboda haka, gwamnatin kasar Sin ta fitar da dokar yaki da ta'addanci a karshen shekarar da ta gabata, kuma dokar ta fara aiki a hukumance daga ranar 1 ga watan Janairun bana.

Ana iya cewa, kasar Sin ta fitar da dokar ne a daidai lokacin da ya dace, saboda ana bukatar wani dandalin yaki da ayyukan ta'addanci a kasar ta Sin a halin yanzu. Duk da haka, Amurka ta yi suka kan dokar, kuma ta bayyana cewa, dokar ba ta da amfani ko kadan, har za ta kawo illa ga 'yancin al'ummar kasar wajen 'yancin fadin albarkacin bakinsu da gudanar da taruruka da kuma bin addinai.

Kamar yadda kuka sani, kullum Amurka tana nuna shakka kan matakan da kasar Sin ta dauka. Yanzu dai, ko da yake ayyukan ta'addanci sun riga sun jefa kasashen duniya da dama cikin mawuyacin hali, amma Amurka ita ma tana ci gaba da nuna shakku kan manufar kasar Sin, kuma ba ta yarda da matakan yaki da ta'addancin da kasar Sin ta dauka ba. Hakan ya bayyana wa duniya karara irin munafuncin kasar Amurkar, sannan hakan ya gwada cewa, Amurkar ba za ta iya jagorantar yaki da ayyukan ta'addanci a tsakanin kasashen duniya ba.

Amurka ta fi mai da hankali ne kan moriyar kanta a ko da yaushe, ta saba da zaben abokai da abokan gaba bisa moriyarta, kuma ta kan yi amfani da ma'auni iri biyu yayin da take gudanar da harkokinta na kasa da kasa, wannan shi ne dalilin da ya sa halin siyasar da yankin Gabas ta Tsakiya ke kara tabarbarewa, kuma shi ne dalilin da ya sa matsalar 'yan gudun hijira a kasashen Turai ya kara kamari, tabbas ne ya kamata Amurka ta sauke nauyin dake bisa wuyanta.

Idan an ce, ana iya yin magana kamar yadda ake so, hakika dai, hakan zai kawo cikas ga ikon fararen hula, amma ba kawo cikas ga ikon masu fada a ji ba.

A baya 'dan takarar zaben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya taba bayyana cewa, za a hana musulmai shiga kasar ta Amurka, wannan ya nuna bambamci da kyama ga mabiya addinin musulunci, kuma hakan ya saba da 'yancin gudanar da addini.

Cikin dogon lokaci, kasashen yamma suna da karfin fada a ji a cikin al'amuran kasa da kasa. Misali, a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, an gamu da hare-haren ta'addanci a Paris da Beirut, kafofin watsa labaran kasashen yamma sun mai da hankali fiye da kima, hakan ya nuna munafuncinsu a bayyane.

To, ina ma'anar 'yancin kan watsa labarai? Ko tana nufin cewar, ana da 'yancin kan zaben wasu mutanen da rayukansu sun fi sauran daraja ke nan?

Wasu gwamnatoci da kafofin watsa labarai na kasashen yamma, ba su yarda da mayarwa masu kai wa fararen hula hari a tashar jirgin kasa ta birnin Kunming na lardin Yunnan dake kudancin kasar Sin 'yan ta'adda ba, duk da cewa, mayakan sun kashe mutane 31, kana mutane 141 suka jikkata a yayin harin da suka kai. A akasin haka kuma, sun amince da wani mutumin wanda ya kashe wani sojin Birtaniya a Landan, kuma yana jiran zuwan 'yan sanda domin kame shi da ya kasance 'dan ta'adda ba tare da tangadi ba.

Ga alamun, ana iya gano cewa, kasashen yamma sun kasa kula da rayukan al'ummomin kasashe masu tasowa, hakan shi ma ya yi wa al'ummomin kasashe masu tasowa gargadi cewa, wajibi ne su yi kokarin kare hakkokinsu.

Kullum ayyukan ta'addanci sun fi kawo masifu ga jama'a da ba su ji ba ba su gani ba, wannan dalilin ya sa gwamnatin kasar Sin take daukan hakikanan matakai domin kare hakkokin al'ummarta, tare kuma da kare tsaron Amurkawa wadanda ke jin dadin bikin kirismeti a unguwar Sanlitun ta birnin Beijing.

Ban da haka, muna fatan Amurka za ta daina nuna kiyayya kan kasar Sin, kuma a maimakon haka, ta fara kokarin yaki da ayyukan ta'addancin dake addabar kasa da kasa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China