in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da samar da kuzari ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2016-03-22 11:09:41 cri

Akwai karin maganar Sinawa da ke cewa, "kada ka ji tsoron hadarin da yake tare hangen nesa, saboda abin da ke nesa ya cancanci a yaba mashi komai wahalar da za'a fuskanta." Duk da haka, da wuya wasu 'yan kallo na kasashen yamma su dauki wannan matsayi game da tattalin arzikin kasar Sin.

Lokacin da tattalin arzikin Sin ke ci gaba da tashinsa a matakin fiye da kashi 10 cikin 100 a shekara guda, wasu masu lura na kasashen yammaci sun dauke shi a matsayin birgewa, da kuma fargaba, sannan suna ganin shi a matsayin wata barazana ga tattalin arkizin duniya. A wani bangaren kuma idan ya ci gaba da tsayawa a kan kashi 6.9 cikin 100 a shekara daya, zai koma ya zauna cikin shiri na nuna ra'ayin ana cikin rikicin tattalin arzikin.

Sai dai kuma a cikin shekaru 30 da suka gabata, masu lura na kasashen yammaci wadanda suke da imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin ba zai ci gaba ba, yanzu sun ji kunya, sannan ba da dadewa ba yadda yanzu haka suke ra'ayin darkushewar tattalin arzikin kasar Sin, zai zama wani abin tarihi.

Me ya sa wadansu masu nazarin suka saba da ra'ayin ci gaban Sin ba zai kai ko ina ba? Ba su san Sin ba ne? ko kuwa suna da wata manufa ne a karkashin hakan?

A kimanin shekaru hudu da suka wuce, Dr. Nouriel Roubini, wani masanin ilmin tattalin arziki ya yi hasashen lalacewar tattalin arzikin kasar Sin, wanda a ganinsa, tattalin arzikin zai fuskanci saurin raguwa a shekarar 2013, abin kuma da bai faru ba a baya. Ba da jimawa ba kuma, George Soros ya bayyana a taron dandalin tattaunawar harkokin tattalin arzikin duniya na Davos cewa, tattalin arzikin kasar Sin na tabarbarewa da sauri, duk da haka, ra'ayin bai samu karbuwa sosai ba a wajen taron, inda Klaus Schwab wanda ya kafa dandalin ya bayyana cewa, "karuwar GDP na kasar Sin da ya kai kashi 6.9% ya kai kimanin adadin GDP na kasar Switzerland gaba daya. A halin da ake ciki yanzu, bunkasuwar tattalin arzikin duniya ya sassauta ga kashi 3%, adadin da ya ragu kwatankwacin kashi 5% a shekarar 2008. Kasar Sin ma tana gyara tsarin tattalin arzikinta, kuma ma iya cewa tana fuskantar makoma mai kyau." Har wa yau, Jim O'Neill wanda ya samar da ra'ayin nan na BRIC a kwanan nan ya bayyana a birnin London cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin da ya kai kashi 6.9% a shekarar 2015 ba karamin ci gaba ba ne, kuma ana samun sauye-sauye masu armashi a tsarin tattalin arzikin kasar ta Sin.

A hakika, a duniyar da muke ciki, kasashen Sin da Indiya ne kawai suke samun karuwar tattalin arziki da ya zarce kaso 6% a shekarar 2015, ga shi kuma yawan tattalin arzikin kasar Indiya ya kai kimanin kashi daya  cikin kashi biyar na tattalin arzikin kasar Sin ne kacal. An kimanta cewa, a shekarar 2015, kasar Sin ta samar da fiye da kashi 25% na karuwar tattalin arzikin duniya. Duk da raguwar farashin mai a duniya, amma ba wai kasar Sin ce ta yi sanadin raguwar ba, kuma yawan danyen mai da kasar ke shigowa daga kasashen ketare ma bai ragu sosai ba.

Masu lura a kasashen yammaci wadanda suke ra'ayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sin matsalolin da kalubale ne kawai suka gano a tattalin arzikin kasar Sin, ba tare da la'akari da nasarorin da kasar ta cimma ba. Ingantuwar tsarin tattalin arzikin kasar Sin da kuma manufofin da ta dauka duk sun shaida dorewar tattalin arzikin ta. Yadda kasar take gyaran tsarin tattalin arzikinta zai iya samar da ingantaccen tushe na bunkasuwar tattalin arzikin duniya, sa'an nan yadda take habaka hadin gwiwar masana'antu da kasashen ketare ma zai iya samar da damar da zuba jari ga kasa da kasa. Alkaluma sun shaida cewa, a shekarar 2015, tsarin tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da ingantuwa, inda yawan kason da sana'o'in samar da hidimomi suka dauka ya karu zuwa kashi 50.5% daga cikin GDP na kasar baki daya, sa'an nan yawan jarin da kasar ta zuba a ketare ya kai yuan biliyan 735 da miliyan 80, wanda ya karu da kashi 14.7%. A zahiri dai, ba tattalin arzikin kasar Sin ke haifar da matsalar tattalin arzikin duniya ba, kuma a maimakon haka, ita ce tana taka muhimmiyar rawar fitar da tattalin arzikin duniya daga mawuyacin hali.(Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China