in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi Allah wadai da hari a masallacin Najeriya
2016-03-18 12:54:38 cri

Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta yi tir da kaddamar da harin kunar bakin wake a wani masallaci a Najeriya.

Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kwamitin AU, ta yi Allah wadai da kaddamar da harin na ranar Laraba a masallaci a birnin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Harin wanda wasu mata 'yan kunar bakin wake su biyu suka kaddamar, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25, kuma ana zargin kungiyar Boko Haram ne da kaddamar da harin.

AU ta jajantawa gwamnatin Najeriyar da al'ummar kasar game da ibtila'in, sannan ta jaddada aniyar ci gaba da amfani da dakarun tsaron kan iyakoki wato MNJTF da suka hada da na tafkin Chadi, da jamhuriyar Benin, don fatattakar kungiyar ta Boko Haram.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China