in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake maido da dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Gambia
2016-03-18 12:08:32 cri


A jiya Alhamis ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwararsa ta kasar Gambia madam Neneh MacDouall Gaye suka sa hannu kan "sanarwar sake maido da huldar dangantakar diflomasiyya tsakanin jamhuriyar jama'ar kasar Sin da kasar Gambia mai bin addinin Musulunci", inda suka shelanta cewa, tun daga jiya Alhamis kasashen biyu sun dawo da huldar dangantakar diflomasiyya tsakaninsu. Sannan a lokacin da suke ganawa da manema labaru bayan da suka yi shawarwari, jami'an kasashen biyu sun bayyana cewa, za su ci gaba da karfafa tushen siyasa na bin matsayin kasancewar Sin daya tak a duniya, kuma za su yi kokari tare wajen tabbatar da ganin an bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu lami lafiya.

A lokacin da suke ganawa da manema labaru tare, Mr. Wang Yi ya ce, dawo da huldar dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Gambia cikin hanzari yana dacewa da moriya da fatan al'ummomin kasashen biyu, kuma yana dacewa da halin da ake ciki a duniya baki daya, har ma yana dacewa da hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Sakamakon haka, an bude sabon shafi game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

"Tsayawa kan matsayin kasancewar Sin daya tak a duniya, yana daga cikin ka'ida da kuma tushen siyasa ga aikin kulla da kuma bunkasa dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. A cikin shekaru biyu da suka gabata, kasar Gambia ta nuna sahihanci da niyya kan wannan batu, kuma ta tsai da kuduri a dai-dai lokacin da ya dace. Bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi tare, daga karshe dai, dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Gambia ta shiga wani muhimmin lokaci."

A nata bangaren, madam Gaye, ministar harkokin wajen kasar Gambia ta ce, sake dawo da dangantakar diflomasiyya tsakanin Gambia da Sin wadda take da makoma mai haske tana da muhimmanci matuka. Bangaren Gambia yana son kara yin hadin gwiwa irin ta moriyar juna tsakaninsa da Sin, kuma zai yi hadin gwiwa da Sin bisa yarjejeniyar da aka cimma a dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka. Gaye ta ce, "Kasashen Sin da Gambia dukkansu sun fahimta cewa, sake dawo da dangantakar diflomasiyya tsakaninsu ta hanyar sake turo da jakadunsu abu ne da ya zama wajibi sosai. Sakamakon haka, bangarorin biyu sun yi namijin kokari ba tare kasala ba ta yadda fatansu ya zama gaskiya bisa ka'idojin girmama wa moriya mafi muhimmanci ta kowane bangare, da kuma kiyaye 'yancinsu"

Gaye ta bayyana cewa, kasar Sin wata muhimmiyar kasa ce a duniya, kuma aminiya ce ga Afirka. Kasar Gambia ta yaba da taimakon da kasar Sin ta dade tana samarwa Afirka, da hadin gwiwar da ta dade tana yi da kasashen Afirka. Gaye ta jaddada cewa, "Jamhuriyar Gambia mai bin addinin Musulunci ta amince da kuma mutunta ka'idar kasancewar Sin daya tak a duniya, tana kuma goyon bayan kokarin dinkuwar kasar Sin baki daya. Gwamnati da jama'ar Gambia za su goyi bayan wannan manufa a duniya, da matakin shiyya-shiyya da kuma a tsakanin kasashen biyu. Mun amince da zaman tare cikin lumana, da ka'idar Sin daya tak a duniya, kuma za mu yi kokarin ganin mun goyi bayan wannan manufa."

Game da lamarin farfadowar dangantaka diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Gambia, Mr. Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya gaya wa manema labaru cewa, "Kowa ya sani cewa, kasar Sin daya tak ce a duniya, kuma babban yanki da yankin Taiwan dukkansu suna cikin kasar Sin ne. Ba mai iya rarraba 'yanci da yankunan kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin na kulla da kuma bunkasa dangantaka a tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana da kasancewar Sin daya tak a duniya."

Lu Kang ya kara da cewa, an sake dawo da dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Gambia ne bisa ka'idojin girmama da amincewa da juna da kuma cin moriyar juna. Bayan sake dawo da wannan dangantaka, bangaren Sin da Gambia za su tattauna kan yadda za a yi hadin gwiwar sada zumunta da kowane bangare zai amfana. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China