160318-Bayani-game-da-motoci-masu-yin-amfani-da-wutar-lantarki-Lami.m4a
|
A watan Disamba na shekarar bara, a cikin wata daya kawai, an yi gargadi sau biyu game da ingancin iska a nan birnin Beijing, sabo da haka, gwamnatin birnin ta gudanar da manufar kayyade yawan motocin dake tafiya a kan hanya. A sakamakon haka, karin mutane suna son sayen motoci masu yin amfani da wutar lantarki. An yi hasashe cewa, yawan motoci masu yin amfani da wutar lantarki da aka saya a wannan shekara a nan kasar Sin zai kai dubu 220 zuwa dubu 250, wanda zai dauki kashi 40 ko fiye cikin dari na duk yawan irin wadannan motocin da aka saya a duk duniya, hakan ya sa, kasar Sin za ta zama kasuwa mafi girma na sayar da motoci masu yin amfani da wutar lantarki.