160314-jawabin-xi-jinping-ya-sa-kaini-kan-ci-gaban-kamfanoni-masu-zaman-kansu-a-sin-jamila.m4a
|
Bisa alkaluman da aka fitar, an ce, adadin tattalin arziki a fannoni masu zaman kan su a kasar ta Sin ya kai kashi 60 cikin dari cikin GDP na kasar, kana adadin harajin da kamfanoni masu zaman kansu suke bugawa ya kai rabin adadin da kasar ta samu. Kana adadin ayyukan yi da suke samarwa ya kai kashi 80 cikin dari a kasar.
Game da wannan, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma shugaban hadaddiyar kungiyar masana'anatu da kasuwanci ta jihar Zhejing dake kudu maso gabashin kasar Sin Nan Cunhui, ya bayyana cewa, kamfanoni masu zaman kansu suna taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arzikin kasar Sin, jawabin da babban sakatare Xi Jinping ya gabatar ya nuna mana cewa, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya sa babbar niyya ga bunkasar tattalin arziki a fannoni masu zaman kan su, hakan ya sa 'yan kasuwa na kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ke cike da imani. Nan Cunhui ya bayyana cewa, "Babban sakatare Xi Jinping ya jaddada cewa, za a kara karfafa aikin aiwawar da manufofin da suke shafar ci gaban kamfanoni masu zaman kansu, hakan zai sa kaimi kan bunkasuwarsu, musamman ma ga 'yan kasuwa. A halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin yana samun bunkasuwa yadda ya kamata, duk da cewa, kila a gamu da wahalhalu a wani lokaci. Kamata ya yi a kyautata manufar raya tattalin arziki, a samar da dammamaki masu dacewa ga kamfanoni masu zaman kansu, ta yadda za su kara ba da gudummawa wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin."
Kana, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, kuma mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masana'antu da kasuwanci ta jihar Jiangsu dake kudancin kasar Sin Yuan Yafei, ya bayyana cewa, tun bayan da aka kammala babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, an fitar da wasu manufofi na raya tattalin arziki a jere a kasar Sin, domin sa kaimi da goyon baya, da kuma ba da jagoranci kan ci gaban tattalin arziki a fannoni masu zaman kan su, saboda tattalin arziki a wannan fanni ba ya samun bunkasuwa cikin sauri a kasar Sin. Amma duk da haka, an fuskanci wasu matsaloli yayin da ake raya tattalin arziki a fannoni masu zaman kan su. Misali abu ne mai wuya a samu jarin da ake bukata, ga karancin kwararrun da ake bukata da dai sauransu. Yuan Yafei yana ganin cewa, idan ana son kubutar da tattalin arziki a fannoni masu zaman kan su daga mawuycin hali, abu mafi muhimmanci shi ne a aiwatar da manufar da ta dace yadda ya kamata. Ya ce, "Ya zama wajibi a aiwatar da manufofin raya tattalin arziki a fannoni masu zaman kan su yadda ya kamata, ta haka ne, za a samar da taimakon da kamfanoni masu zaman kansu ke bukata. Wato ya fi dacewa a samar da taimako bisa bukatun kamfanonin, bayan da aka yi bincike da kuma zabe."
Ban da haka, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, yana fatan 'yan kasuwa za su kara kyautata hallayensu, tare kuma da kyautata tsarin tafiyar da harkokin kamfanoninsu, ta yadda za su samu ci gaba yadda ya kamata. (Jamila)