160311-Ina-raayinku-kan-rahoton-aikin-gwamnatin-kasar-Sin-Lubabatu.m4a
|
A safiyar Asabar da ta gabata, wato 5 ga wata, aka kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda firaministan kasar Sin Li Keqiang a madadin gwamnati ne ya gabatar da rahoton aikin gwamnati ga mahalarta taron, inda kuma baya ga waiwayen aikin da gwamnati ta gudanar a shekarar da ta gabata, aka kuma fitar da matakan yadda gwamnatin kasar za ta sauke nauyin dake wuyanta a shekarar 2016. To, ina ne ra'ayinka game da rahoton? A biyo mu cikin shirin, don sauraron ra'ayoyin bangarori daban daban.(Lubabatu)