160309.m4a
|
Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron mambobin kungiyar masu da'awar raya tsarin dimokuradiyya ta kasar Sin da na sassan masana'antu da cinikayya, wadanda ke halartar taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin wato CPPCC dake gudana a nan birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, ya kamata a nace ga bin babban tsarin tattalin arzikin kasar Sin, tare da kara azama ga ci gaban nau'o'in tsare-tsaren tattalin arziki.
A jawabin da ya gabatar yayin taron mambobin majalisar CPPCC da kungiyar masu da'awar raya tsarin dimokuradiyya ta kasar Sin da na sassan masana'antu da cinikayya ta halarta, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, duk da tinkarar halin duniya mai sarkakiya da kuma babban aikin yin kwaskwarima da neman samun ci gaba a gida da aka yi, kasar Sin ta samu saurin ci gaba a fannin tattalin arziki, har ma yawan karuwarsa ya kasance a sahun gaba a duniya, baya ga karfafa ci gaban aikin gyare-gyare, da samun babbar bunkasuwar tattalin arziki da siyasa da al'adu da zamantakewar al'umma da ma muhallin halittu. Hakan ya sa kasar Sin ta kammala kusan dukkan burin da aka kuduri aniyyar cimmawa a bara, tare da dasa wata kyakkyawar aya ga shirin ci gaban kasar Sin na shekaru biyar biyar karo na 12.
Ban da haka, shugaba Xi Jinping ya ba da wasu shawarwari kan yadda za a gaggauta ci gaban kasar Sin, inda ya bayyana cewa, da farko ya kamata a tsaya tsayin daka kan bi da kyautata babban tsarin tattalin arzikin kasar Sin irin na gurguzu. Aiwatar da tsarin tattalin arziki na mallakar abubuwan kawo albarka ga gwamnati tare da bunkasa nau'o'in tsare-taren tattalin arziki, wannan wata babbar manufa ce da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta tsara, wanda ya kasance wani muhimmin bangare na tsarin gurguzu da ke da halin musamman na kasar Sin, kuma wata bukata ce ta kyautata tsarin harkokin kasuwanci iri na gurguzu.
Tsarin tattalin arziki mai zaman kansa kuma wani tsari ne da aka kafa tun bayan da kasar Sin ta fara bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida a shekarar 1978 bisa inuwar manufofin JKS. Shugaba Xi ya jaddada cewa, tsarin tattalin arziki mai zaman kansa na da muhimmin matsayi a cikin aikin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin, don haka za a ci gaba da ba da kwarin gwiwa wajen raya wannan tsari, tare da yin kokarin samar da kyakkyawan muhalli wajen raya ayyukan tattalin arziki da ba na gwamnati ba. Bugu da kari, ya kamata a daidaita tsarin tattalin arziki na gwamnati da wanda ba na gwamnati ba yadda ya kamata, domin su taimakawa juna, a maimakon kawo illa ga juna.
Shawara ta biyu da shugaba Xi ya bayar ita ce, ya kamata a aiwatar da matakan sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki mai zaman kansa lami lafiya. Shugaba Xi ya ce, a 'yan shekarun baya baya nan, JKS da gwamnatin kasar Sin sun bullo da jerin matakai don raya tsarin tattalin arziki mai zaman kansa. Musamman ma bayan babban taro karo na 18 na JKS, sakamakon zurfafa aikin yin gyare-gyare daga dukkan fannoni, wadannan matakai sun samu kyautatuwa. Amma a halin yanzu, ya kamata a dora muhimmanci a wadannan fannoni. Na farko, a yi kokarin warware matsalar hada-hadar kudi da kanana da matsakaitan masana'antu ke fuskanta, bisa hanyar kyautata tsarin hada-hadar kudi. Na biyu, a kara yawan sana'o'i da ayyukan da za a amince don zuba jari a cikinsu. Wato game da dukkan sana'o'i da fannonin da doka ta amince da su, ya kamata a kara kwarin gwiwa wajen zuba jari a bangaren sassa masu zaman kansu. Na uku, a gaggauta raya tsarin ba da hidima ga jama'a, da goyon bayan masana'antu masu zaman kansu ta fuskar fasahohi. (Kande Gao)