160307-shugaban-hukumar-kwastam-ya-ce-bako.m4a
|
A ranar 3 ga wata, yayin da shugaban hukumar kwastam ta Nijeriya Hameed Ibrahim Ali ya zanta da wakilinmu Bako, ya ce, ya kamata a inganta hadin gwiwa da hukumar kwastam ta kasar Sin don kawo sauki ga cinikayyar bangarorin biyu.
Malam Hameed ya fadi hakan ne yayin da ya halarci taron kara-wa-juna-sani game da harkokin kwastam dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, ya ce, Nijeriya tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin don raya harkokin kwastam ta hanyar sadarwar zamani, wannan zai iya magance cin hanci da rashawa da kawar da aika-aikar dake tsakanin mutum da mutum, kuma yana fatan kara mu'amala da kasar Sin game da mutane da na'urorin zamani da kirkiro da sabbin abubuwa, kana kasashen biyu za su hada gwiwa don yaki da lafuffukan dake shafar kwastam a tsakaninsu.(Bako)