Jaridar Cameroon Tribune ta ba da labari cewa, an fara shirin musayar 'yan jaridu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika na shekarar 2016 a nan birnin Beijing, manema labaru fiye da 19 da suka fito daga kasashen Afrika dabam dabam, sun fara samu horo da yadda ake nemo labarai a cikin watanni 10 masu zuwa a kasar Sin. An gudanar da wannan aiki ne domin kara wa manema labaru na kasashen Afrika sani kan bunkasuwar hulda a tsakanin Sin da kasashen Afrika da kuma yada labarai game da hadin gwiwar bangarorin biyu. Ban da haka kuma, wadannan manema labaru na kasashen Afrika za su kara sani kan manufofin harkokin waje da kuma bunkasuwar da kasar Sin ta samu a dukkan fannoni, kana za su kai ziyara a wurare daban daban na kasar Sin.(Lami)