Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya shiga ganawar wakilan birnin yayin da suke duba rahoton aikin gwamnati jiya Asabar a taron shekera-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar. Ya ce, kamata ya yi birnin na Shangahai ya yi amfani da karfinsa da kuzarin da yake da wajen kirkiro hanyoyin da za a kara zurfafa yin gyare-gyare.
Shugaba Xi ya kara da cewa, an zabi birnin Shanghai ya zama yankin cinikayya cikin 'yanci na farko na kasar wato FTZ kasancewarsa cibiyar harkokin kudi da cinikayya. Sannan masu tsara manufofi na kasar sun yi amfani da shi wajen gwada sabbin manufofin kasar ta fuskar sarrafa kudade hannayen jari matakin da zai tantance irin kamfanonin waje da za su zuba jari a ciki.
Da ya juya ga irin kokarin da birnin na Shanghai ke yi a bangaren gyare-gyare kuwa, shugaba Xi ya ce, yana fatan birnin zai kara zurfafa gyare-gyare ta hanyar mayar da hankali ga yankin cinikayya cikin 'yanci na gwaji da kasar Sin ta bullo da shi.
Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi a yi amfani da wannan shiri na FTZ wajen gwada hanyoyin kirkire-kirkire. Ya kuma bukaci birnin na Shanghai da ya kasance a kan gaba wajen kirkiro yanayin harkokin kasuwancin na kasa da kasa da ya dace kamar yadda doka ta tanada, matakin da shugaba Xi ya ce zai samar da daidaito tare da yanayin kasuwa mai inganci.(Ibrahim)