160302-Muhimman-taruka-biyu-na-kasar-Sin-na-shekarar-2016-Sanusi.m4a
|
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, majalisa ce da ta kunshi mambobi daga sassa daban-daban na kasar da suka hada da jam'iyyun siyasa, kungiyoyi da wakilai masu zaman kansu.
Bisa al'ada, jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar ce ke da wakilai mafi rinjaye a majalisar, inda take da kashi 1 bisa 3 na daukacin mambobin majalisar. Sauran mambobin majalisar sun fito ne daga jam'iyyun da ke kawance da jam'iyyar kwaminis mai mulki da sauran wakilai masu zaman kansu wadanda ba sa cikin kowace jami'yya.
A daya hannun kuma majalisar wakilan jama'a wato NPC a takaice majalisa ce da ake zaben wakilanta daga mazabun gundumomin, yankuna masu 'yancin gashin kansu, birane karkashin kulawar gwamnatin tsakiya, rundunar sojojin kasar.
Aikin majalisar wakilan sun hada da gyaran kundin tsarin mulkin kasa da sanya ido wajen ganin an aiwatar da tanade-tanaden da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Bugu da kari, aikin majalisar ce ta bullo da dokoki da suka shafi manyan laififfuka, harkokin jama'a, hukumomi da ma'aikatun gwamnati da sauran batutuwan da ke shafar rayuwar Sinawa.
Har ila, majalisar wakilan ce take zabe da kuma nada wadanda za su jagoranci hukumomin gwamnati da yanke hukunci game da manyan batutuwan da suka shafi kasa baki daya.
Masana na bayyana cewa, kamar yadda aka saba a tarukan na bana ma, ana sa ran a tattauna muhimman batutuwa kamar, shiri na 13 na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki, da harkokin tattalin arziki na shekarar 2016, manufofin diflomasiyar kasar Sin, shirin nan na "ziri daya da hanya" da dai sauransu. (Ibrahim, Saminu, Ahmad/Sanusi chen)