160217-Gwamnatin-kasar-Sin-ta-gabatar-da-takarda-ta-farko-game-da-matakan-daikile-hadarin-nukiliya-Sanusi.m4a
|
Alkaluma na nuna cewa, wutan lantarkin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da makamashin nukiliya makamashi shi ne mafi tsabta da kuma inganci. A halin da ake ciki yanzu, injunan samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya a babban yankin kasar Sin sun kai 30, a inda suke samar da wutar lantarki da yawansa ya kai kilowatts miliyan 28.31, ban da haka, injunan da ake kafawa a halin yanzu sun kai 24, yawansu ya kasance a sahun gaba a duniya.
Masana sun bayyana cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake kokarin raya fasahar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya shi ne tabbatar da tsaron aikin a ko da yaushe.
Takardar da gwamnatin kasar Sin ta fitar game da yadda za a dakile aukuwar hadarin dake shafar nukiliya, ita ce takarda ta farko da kasar ta Sin ta fitar a tarihi, kuma ta kunshi fannoni takwas, inda musamman ta yi bayyani kan yadda kasar Sin ta dauki matakai domin dakile hadarin da kuma sakamakon da kasar ta samu a wannan fannin.
A kokarin ganin haka ta cimma ruwa a wannan fannin, yanzu haka an kafa tawagogin kwararru guda 25 dake kunshe da ma'aikata daga sassan sana'o'i daban-daban sama da 1300, ban da haka kuma za a kafa wata tawaga ta musamman mai wakilai 320 domin samar da agajin gaggawa a duk lokacin da aka samu hadurran da ke da nasaba da nukiliya. (Ibrahim, Mamane Ada, Saminu Alhassan, Sanusi Chen)