160210-Kasar-Sin-na-shirin-kara-inganta-Ishorar-lafiyar-alumma-Sanusi.m4a
|
An cimma wannan matsaya ce yayin taron kiwon lafiya da shirin daidaita iyali na shekarar 2016 da aka shirya a kwanakin baya.
Bugu da kari, za a kyautata tsarin ishorar kiwon lafiya na al'umma da ba da aikin jinya bisa matakai daban-daban, baya ga sabbin matakai da za a dauka wajen ganin an aiwatar da tsarin nan na haifar yara biyu a fadin kasar.
Bayanai na nuna cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta dauki kwararan matakai da dama wajen yin gyare-gyare kan harkokin kiwon lafiya da ba da jinya. Sakamakon haka, kasar Sin ta cimma burin da MDD ta tsara shekaru biyar da suka gabata a shirin neman ci gaba a shekarar 2000 dangane da yawan kiyasin tsawon rayuwar jama'a a duniya da yawan mutuwar mata masu juna biyu da yawan mutuwar jarirai da wasu sauran muhimman adadin dake da nasaba da lafiyar jama'a.
Masu sharhi na cewa, wannan mataki wata alama ce da ke nuna yadda mahukuntan kasar Sin suke ba da muhimmanci ga lafiyar al'ummominsu.
Masu iya magana na cewa, lafiya uwar jiki, kuma muddin al'umma a kasa na cikin koshin lafiya, ko shakka babu, za su kara zage damtse wajen ba da tasu gudummawar ga ci gaban kasa. (Ibrahim Yaya, Mamane Ada, Saminu Alhassan, Sanusi Chen)