in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya kammala ziyarar aiki a kasashe hudu na kudancin Afirka
2016-02-06 14:04:12 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyarar aiki a kasashe guda hudu dake kudancin Afirka, na tsawon mako daya tare da kammalawa a Asabar din nan 6 ga watan Fabrairu, domin aiwatar da shiri guda 10 game da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka wadanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tsara a yayin ziyararsa a Afirka.

Domin da maimaita manufar diflomasiyyar kasa ta Sin ta gargajiya, ministan harkokin wajen na kasar Sin ya kai ziyarar aiki a kasashen Afirkan a farkon watan sabuwar shekara.

A ranar Jumma'ar nan 5 ga wata kuma, Wang Yi ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Namibia, da ta kasance ta karshe ta ziyarar aikinsa a nahiyar, inda ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, ko da yake kasashen hudu da ya ziyarta suna cikin bambancin yanayi na samun bunkasuwa, amma kowace kasa tana da kwarewar kanta, haka kuma, dukkansu sun yaba wa shirin goma da shugaba Xi Jinping ya tsara wajen yin hadin gwiwa, suna kuma sa ran shiga cikin shirin.

Bugu da kari, cikin ziyararsa a kasashen, an tattauna yadda za a iya yin hadin gwiwa bisa bukatu da kuma hanyoyin bunkasuwar kasashen bisa shirin, domin samun sakamako masu gamsarwa.

Dangane da hakan, ga cikakken bayani da wakilinmu Sanusi Chen zai karanto mana:

A safiyar ranar Jumma'a 5 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya isa kasar Namibiya, watau kasa ta karshe a ziyarar aikinsa a kudancin Afirka, inda ya gana da mataimakiyar firaministan kasar, kana ministar dake kula da dangantaka da hadin gwiwar kasa da kasa Netumbo Nandi Ndaitwah.

A yayin ganawarsu, madam Ndaitwah ta ce, "A shekarar 2014, gaba daya kasar Sin ta zuba jari a ma'adinan uranium dake yankin kasar Namibia na dallar Amurka biliyan 5, lamarin da ya nuna babban taimako da goyon baya da kasar Sin ta samar wa kasar Namibiya. Haka kuma, ana ci gaba da kyautata ayyukan da abin ya shafa, kasar Namibiya ta gamsu sosai dangane da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu."

Bayan da ya yi shawarwari tare da ministar harkokin waje ta kasar Namibiya, shugaban kasar Hage Gottfried Geingob ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi.

A tattaunawarsu, Shugaba Hage Gottfried Geingob ya ce yana son kasar Sin sosai, kasancewarta kasa mai girma, kuma ganin yadda ministan harkokin waje Wang Yi ya kai ziyara a karamar kasar kamar Namibiya, ya shaida zumuncin dake tsakanin kasashen biyu da kuma huldar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, sannan hadin gwiwa a fannin tattalin arziki a tsakaninsu ya kawo moriya ga kasar Namibiya. Shugaba Hage Gottfried Geingob ya ce, "Muna ganin cewa, kasar Namibiya daya ce daga cikin wasu kasashen Afrika da za su iya yin hadin gwiwa mai inganci tare da kasar Sin, mun samu moriya sosai daga taimakon da kasar Sin ta yi mana a fannonin raya masana'antu da samar da fasahohi da kara guraban ayyukan yi."

A cewar ministan, manufarsa ta ziyarar kasar ta Namibiya ita ce, tsara hakikanin matakai na yin hadin gwiwa da Sin da Namibiya, bisa manyan shirye-shirye 10 da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar dangane da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, ta yadda za a samu sakamako mai kyau daga dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Namibiya, tare da taimakawa Namibiya raya kanta bisa dimbin albarkatun kasa. Mr. Wang Yi ya ce, "Bisa tanade-tanaden da ke cikin manyan shirye-shiryen 10, mun tabbatar da hanyar da Sin da Namibiya za su bi da muhimman fannoni da za mu mai da hankali a kai a nan gaba a fannin yin hadin gwiwa a tsakaninmu. Alal misali, za a warware matsalar rashin isasshen wutar lantarki da ke fi adabar Namibiya ta hanyar yin hadin gwiwa ta fuskar yin amfani da karfin iska da hasken rana wajen samar da wutar lantarki. Za a taimakawa Namibiya samun karin sabbin fannonin raya tattalin arziki ta hanyar yin hadin gwiwa ta fuskar harkokin teku da tashar jirgin ruwa. Kana kuma za a tabbatar da ganin Namibiya ta samu isasshen abinci ta hanyar inganta hadin gwiwa ta fuskar aikin gona da yin musayar fasahar aikin gona."

A cikin kasashe 4 da ya ziyarta, minista Wang ya yi shawarwari da shugabannin wadannan kasashe bisa yanayin da kasashensu ke ciki, don gudanar da shirin hadin gwiwa a fannoni 10 tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da shugaban Xi ya gabatar.

A zango na farko wato Malawi, minista Wang ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa a fannonin aikin gona, kirkire-kirkire, da muhimman ababen more rayuwa, da horar da mutane da kiwon lafiya tsakaninsu, don cusa sabon kuzari wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a wurin.

A kasar Mauritius dake yankin gabashin kasashen Afrika, Wang Yi ya gabatar da cewa, ya kamata a yi amfani da fiffikon matsayi na musamman na kasar da ke nahiyar Afrika, don gina kasar da ta zama wata kofar da Sin za ta zuba jari da inganta cudanya da kasashen Afrika, da inganta hadin gwiwa a fannonin hada-hadar kudi, da zirga-zirgar jiragen sama da hadin gwiwar tattalin arziki a fannin teku.

A kasar Mozambique ma, Sin ta gabatar da inganta hadin gwiwa da kasar a fannin masana'antu da aikin gona.

Wang Yi yana mai cewa, "Shugaba Xi Jinping ya gabatar da shirye-shirye 10 na hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka don taimakawa kasashen Afirka da su gaggauta bunkasa tattalin arziki a fannoni daban daban, da raya masana'antu, da inganta karfinsu na raya kasa, ta haka za a taimaka musu daga tushe wato kawar da mawuyacin hali na fuskantar tasirin da sauyin farashin kayayyakin danye ya yi musu."

Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai kan matsayinta da rawarta a idon nahiyar Afirka. Koda yake Sin ta samu bunkasuwa, amma ta kiyaye zama tare da kasashen Afirka da kuma sauran kasashe masu tasowa. Ta haka za a samu duniya mai zaman lafiya da adalci, da kuma kasashen za su samu bukasuwa tare a dukkan fannoni. (Tasallah, Zainab, Lami, Bako, Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China