in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An koyar da al'adun bikin sabuwar shekarar Sinawa a Afirka ta kudu
2016-02-04 10:42:03 cri
Ofishin jakadancin Sin da ke kasar Afrika ta Kudu, da makarantar confucius da ke Pretoriya a ,kasar sun shirya taron koyar da al'adun bikin sabuwar shekarar Sinawa a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Afrika ta Kudu da ma'aikatar kula da cinikayya da masana'antu.

Bikin da aka yi tsakanin ranakun talata 2 ga wata da laraba 3 ga watan nan ya samu halartar manyan jami'ai sama da 90 da suka fito daga ma'aikatar harkokin waje da ma'aikatar cinikayya da masana'antu, da ma'aikatar sufuri, da hukumar kwastam da sauran hukumomi.

An kirkiro da sabbin tunani na shirya taron koyar da al'adu game da bikin sabuwar shekarar Sinawa, don kara fahimtar da mutane a sassan daban daban game da al'adun kasar Sin, ta yadda za a inganta tushen hadin gwiwar kasar Sin da Afrika ta Kudu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China